Buhari karya ya sharara mana akan takardun shi na makaranta - Atiku

Buhari karya ya sharara mana akan takardun shi na makaranta - Atiku

- Jam'iyyar PDP da dan takarar ta Alhaji Atiku Abubakar sunce idan har shugaba Buhari ba karya ya sharara ba to ya fito da takardun shi da ya ce ya mallaka

- Jam'iyyar ta kuma umarce shi da ya tilasta hukumar soji ta fito da takardun na shi tunda ya yi aiki a karkashin ta shekaru da dama

Jam'iyyar PDP da dan takarar ta a zaben shugaban kasa da aka gabatar watannin da suka gabata, Alhaji Atiku Abubakar, sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da sharara karya akan takardun shi na makaranta.

Bayan haka kuma jam'iyyar da dan takarar na ta, sun zargi cewa shugaban kasar ya yi wani ikirari a lokacin da ya ke amsa tambayoyin da suka gabatar a kotun daukaka kara ta zaben shugaban kasa, inda ya ce yafi Atiku cancanta da mulkin Najeriya. Jam'iyyar ta karyata wannan ikirari da shugaban kasar ya yi.

Buhari karya ya sharara mana akan takardun shi na makaranta - Atiku

Buhari karya ya sharara mana akan takardun shi na makaranta - Atiku
Source: Depositphotos

Sun bayyana cewa, ba kamar Atiku ba, har yanzu shugaban kasar ya kasa nuna takardun shi na makaranta, wanda ya ce ya mallaka.

Jam'iyyar PDP din da dan takarar ta Atiku Abubakar sun taso da wannan magana ce a madadin raddi ga abinda shugaba Buharin ya fada.

Sun je kotun ne domin su kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa da ya gabata, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyarsa APC suka samu nasara.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi

A wata amsa da jam'iyyar ta gabatar a ranar 15 ga watan Afrilu, wanda lauyoyin jam'iyyar karkaashin jagorancin Livy Uzoukwu (SAN), jam'iyyar PDP da Atiku sun yi ikirarin cewa rashin gabatar da takardun da shugaban kasar ya yi yana nuna cewa ya sharara wa mutane karya ne akan takardun na shi.

Jam'iyyar ta kalubalanci shugaban kasar, a matsayin sa na shugaban kasa mai iko, kuma babban kwamandan sojojin Najeriya, da ya sanya hukumar soji ta kasar nan, inda ya yi aiki da su da, domin su gabatar da takardun da ya yi ikirarin ya na da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel