Ekiti ba zata zama karshe ba wurin kaddamar da biyan sabon mafi karancin albashi, inji Fayemi

Ekiti ba zata zama karshe ba wurin kaddamar da biyan sabon mafi karancin albashi, inji Fayemi

-Bada dadewa ba zamu fara biyan mafi karancin albashin N30,000, inji Fayemi

-Ba za'a barmu baya ba wurin biyan sabon mafi karancin albashi, inji gwamnatin jihar Ekiti

Gwaman jihar Ekiti Kayode Fayemi ya yiwa ma’aikatansa alkawarin cewa jihar Ekiti ba zata kasance karshe ba wurin kaddamar da biyan sabon mafi karancin albashin N30, 000 ba.

A jawabinsa ta bakin mataimakinsa Bisi Egbeyemi, gwamnan ya taya kungiyoyin kwadago murnar samun sabbin shugabanni.

Ekiti ba zata zama karshe ba wurin kaddamar da biyan sabon mafi karancin albashi, inji Fayemi

Ekiti ba zata zama karshe ba wurin kaddamar da biyan sabon mafi karancin albashi, inji Fayemi
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto

Gwamnan ya tabbatarwa ma’aikatan cewa baza suyi kasa a gwiwa ba wurin kaddamar da biyan mafi karancin albashin N30,000 a jihar.

“ Kowane ma’aikacin kasar nan na jiran ya fara samun sabon mafi karanci albashin. Da yardar Allah Ekiti ba zata kasance a sahun baya ba wajen fara biyan albashin. Domin yin haka zai karawa ma’aikata karfin yin aiki yadda ya dace.” Inji gwamnan.

Fayemi wanda ya bayyana jindadin ma’aikata a matsayin daya daga cikin manufofin gwamnatinsa, yace tabbas duk wani hakki da ma’aikatan ke bin gwamnatin yana na tafe zuwa garesu. Abinda kawai nake so daga wajenku shine jajircewa yayin gudanar da ayyukanku domin ciyar da jiharmu gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel