Gwamnoni na fakewa da matsalar tsaro suna satar kudaden al’umma – Inji Magu

Gwamnoni na fakewa da matsalar tsaro suna satar kudaden al’umma – Inji Magu

Shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa akwai gwamnonin da suke fakewa da matsalolin tsaro a jahohinsu suna wawuran kudaden jama’a.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Magu ya bayyana haka ne yayin taron gogar da sabbin gwamnonin Najeriya da kungiyar gwamnonin Najeriya ta shirya a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kashe masu yankan itace 14 a dajin Borno

Magu yace halin rashin tsaro da ake fama dashia a yanzu haka ya baiwa wasu gwamnoni daman sace kudaden al’umma cikin sauki ba tare da jama’a yan Najeriya sun ankara ba, don haka a wajensu babbar dama ce wannan.

“Muna da hujjoji dake nuna yadda wasu gwamnoni suke wawuran kudaden jahohinsu da sunan magance matsalar tsaro, haka zalika akwai batutuwan da muke samu na cewa wasu gwamnoni da kansu suke shirya matsalolin tsaron a jahohinsu kawai don su kara kudaden tsaronsu.” Inji shi.

Su dai kudaden tsaro wasu kudi ne da kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince ma gwamnoni su kashesu akan duk wata matsalar tsaro ba tare da sun bukaci amincewar majalisun dokokinsu, kuma babu wanda ya isa ya tambayesu yadda aka kashesu.

Don haka Magu ya ja kunnen sabbin gwamnoni dama wadanda zasu zarce akan kujerunsu dasu kasance masu tsantseni da kula da adalci wajen kashe kudin al’umma a matsayinsu na shuwagabannin tsaron jahohinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel