Gwamnan Bayelsa da Katsina sun yi magana a kan batun karin albashi

Gwamnan Bayelsa da Katsina sun yi magana a kan batun karin albashi

Mai girma Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa yayi magana a game da batun karawa Ma’aikata albashi, inda yace akwai abin da yake jira kafin ya fara biyan ma’aikatansa akalla N30, 000.

Seriake Dickson ya bayyana cewa yana jiran shawara daga bakin hukumar da ke kula da harkar albashin ma’aikata a Najeriya domin ta tsaga masa yadda zai biya ma’aikatan da ke aiki a gwamnatin jihar abin da bai gaza N30, 000 ba.

Gwamna Seriake Dickson yayi wannan jawabi ne a Ranar bikin ma’aikata da aka yi jiya, 1 ga Watan Mayun 2019. Gwamnan yace ya dade cikin sahun masu neman a karawa Ma’aikata albashi zuwa akalla N30, 000 duk wata tun ba yau ba.

KU KARANTA: Ma'aikatan Kogi sun ba Gwamna Bello wasu sharudan zarcewa

Gwamnan Bayelsa da Katsina sun yi magana a kan batun karin albashi

Gwamna Masari yace zai yi kokarin kara albashi a Katsina
Source: UGC

Gwamnan na jihar Bayelsa yace yana goyon bayan wannan batu na karawa ma’aikata albashi zuwa N30, 000, amma yana mai jiran shawara daga hukumar nan ta National Income and Wages Commission kafin ya soma biyan ma’aikata sabon albashin.

A jihar Katsina kuma, Gwamna Aminu Bello Masari ya fito ya bayyana cewa ba zai iya cewa zai iya biyan wannan kudi, ko ba zai iya ba. Gwamnan na APC yace akwai bukatar su zauna da kungiyar kwadago na NLC domin su nemi maslaha a jihar.

Rt. Hon. Aminu Masari ya bayyana wannan ne a lokacin da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati na jihar Katsina, Idris Tune, ya wakilce sa wurin taron Ranar ma’aikata da aka shirya Ranar Larabar nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel