Ranar kin dillanci: Ma’aikatan Kogi sun gindaya ma Yahaya Bello sharadin samun goyo baya a zaben gwamna

Ranar kin dillanci: Ma’aikatan Kogi sun gindaya ma Yahaya Bello sharadin samun goyo baya a zaben gwamna

Kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jahar Kogi ta bayyana cewa ma’aikata ne zasu tabbatar da wanda zai lashe zaben gwamnan jahar Kogi a zaben da zai gudana na ranar 2 ga watan Nuwamba, kamar yadda shugaban kungiyar ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban NLC na jahar, Onu Edoka ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya daya gudana a babban filin wasa dake garin Lokoja, babban birnin jahar Kogi.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kashe masu yankan itace 14 a dajin Borno

Ranar kin dillanci: Ma’aikatan Kogi sun gindaya ma Yahaya Bello sharadin samun goyo baya a zaben gwamna

Yahaya Bello
Source: UGC

A jawabinsa, Mista Edoka yace idan har hukumar zabe mai zamanta ta kasa, INEC, zata yi adalci a zaben gwamnan jahar dake karatowa, toh tabbas kuri’un ma’aikatan jahar ne zasu tabbatar da wanda zai zama gwamnan jahar.

Don haka Edoka ya gindaya ma Gwamna Yahaya Bello sharadin samun goyon bayan ma’aikatan jahar, inda yace akwai bukatar ya fara biyan dukkanin basussukan da suke binsa a cikin dan kankanin lokaci.

“Idan har ka biyamu albashinmu, ka biyamu alawus din hutu, sa’annan ka tabbatar da karin girman ma’aikata, shikenan mu kuma zamu tsaya da kai tsayin daka har sai ka maimaita wa’adin shekaru hudu a mukamin gwamna.” Inji shi.

Edoka ya jaddada cewa ma’aikata na bin gwamnatin Kogi bashin albashi na watanni bakwai zuwa watanni 30, don haka yayi kira ga gwamnatin data dana watsa farfaganda ta tsaya ta fuskanci matsalar da yadda zata shawo kanta.

Sai dai a hannu guda, Gwamna Yahaya ya musanta batun bashin albashin watanni 30 da NLC tayi, inda yace albashin watanni biyar kacal ma’aikata ke binsa, kamar yadda ya bayyana ta bakin wakiliyarsa a wajen bikin, sakataren gwamnati, Folashade Ayoade-Arike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel