Gwamnatin Kebbi bata da matsaya akan biyan mafi karancin albashin N30,000

Gwamnatin Kebbi bata da matsaya akan biyan mafi karancin albashin N30,000

-Babu tabbas! Gwamnatin jihar Kebbi ba tace zata biya mafi karancin albashin N30,000 ba

-Ma'aikatan Kebbi basu san ya mafi karancin albashin zai kaya da su ba a jihar tasu

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi yace gwamnatinsa zata ba wannan sabon mafi karancin albashin N30,000 irin kulawar da ta dace. Gwamnan dai yayi wannan jawabin ne ranar Laraba yayinda da ake bikin ranar ma’aikata.

“ Ma’aikta sune kashin bayan cigaban tattalin arziki a don haka walwalarsu abin kulawa a wajen gwamnatinmu.

Gwamnatin Kebbi bata da matsaya akan biyan mafi karancin albashin N30,000

Gwamnatin Kebbi bata da matsaya akan biyan mafi karancin albashin N30,000
Source: UGC

KU KARANTA:Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto

“ Bamu bada tabbacin cewa zamu biya albashin ba a daidai lokacin da ake tsanmaninsa, amma sai dai dukkanin hakokan ma’aikatan zamu bada akan lokaci”, Bagudu yayi sharhi.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar ya wakilta wato Ahaji Babale Umar ya lura cewa a kullum ma’aikatan jihar raguwa sukeyi inda suke barin aikin gwamnatin.

Umar ya kara da cewa kawowa yau gwamnati ta dauki kwararrun malamai 2000 domin maye gurbin wadanda suka bar aikin.

Ya kuma roki ma’aikatan da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukan ba tare da kuya ba domin shine kadai zai iya ba jihar tasu cigaban da suke bukata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel