Buhari ya sauyawa ma’aikantasa wurin aiki kafin a rantsar dashi a karo na biyu

Buhari ya sauyawa ma’aikantasa wurin aiki kafin a rantsar dashi a karo na biyu

-Wasu ma'aikata sun samu sauyin wuraren aiki gabanin a rantsar da Buhari a karo na biyu

-Kimanin ma'aikata 71 ne wannan musayar ta shafa, zance daga fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari ya aminta da sauyin wuri aiki na ma’aikata 71 dake fadar shugaban kasa a Abuja, tun kan a rantsar dashi a karo na biyu.

Wata takardar da ta fito daga ofishin shugaban ma’aikata na kasa ta bayyana cewa ma’aikata 71 ne sauyin zai shafa wanda suka hada da ma’aikatan tsaro da kuma na farin kaya.

Buhari ya sauyawa ma’aikantasa wurin aiki kafin a rantsar dashi a karo na biyu

Buhari ya sauyawa ma’aikantasa wurin aiki kafin a rantsar dashi a karo na biyu
Source: Twitter

KU KARANTA:Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto

Takardar wacce Daraktan zirga-zirgar ma’aiktan ya sanya ma hannu wato M. S Naibi tace dukkanin sauye-sauye dai za’a kammalasu ne zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Mayu.

Inda ya kara da cewa ma’aiktan da abin ya shafa suyi shirin karbar aikin nasu a haka ko kuma sabanin hakan na iya jawo masu matsala.

Wadanda aka sauyawa wurin aikin dai an dauke sune zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya, na shugaban ma’aikata na kasa da kuma wasu daga cikin ma’aikatun gwamanati.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel