Awon gaba: Yadda ake yiwa masu tafiya Saudiyya cushen kaya a filin jirgin Mallam Aminu Kano

Awon gaba: Yadda ake yiwa masu tafiya Saudiyya cushen kaya a filin jirgin Mallam Aminu Kano

A yayinda har yanzu jama'a ke cigaba tofa albarkacin bakinsu a kan halin da matashiyar nan, Zain Habib Aliyu, ta shiga a hannun hukumomin Saudiyya bayan an kama ta bisa zargin safar kwaya zuwa kasar, Yassir Ramadan Gwale, wani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum, ya warware zare da abawa a kan yadda wasu ma'aikata a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ke yin wani mugun hali da suke kira 'awon gaba'.

Ga abinda Yassir din ya ce: "masu zuwa aikin umra musamman wanda suke tashi daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano, suna yin awon gaba da kaya da jakunkunan mutane, sun sani ko basu sani ba.

Dukkan ma'aikatan da suke aiki a filin jirgin saman Kano musamman masu lura da yadda ake auna kaya, sun san yadda ake goyawa fasinjoji kayan da ba nasu ba a jikin tikitinsu.

Wannan ba sabon abu bane a filin jirgin saman Kano. Kai fasinja da zaka tashi matukar kayanka basu cika kilon ka ba, to za a sanya ka kayi awon gaba da abinda baka sanshi ba, kuma ba zaka taba sani ba indai kayan lafiya lau suke.

Kuma kai fasinjan da aka dorawa kayan da kayi awon gaba baka sani ba, ba zaka taba fahimtar cewa an goya maka wani kayan da baka sanshi ba, sai dai idan matsala ta auku sannan ne zaka sani, dn za a bibiyi tikitin da kayan ke dauke da shi.

Awon gaba: Yadda ake yiwa masu tafiya Saudiyya cushen kaya a filin Mallam Aminu Kano

Filin jirgi na Mallam Aminu Kano
Source: Depositphotos

Amma wadan da suka yi abin da wanda zai dauki kayan idan anje can Jedda duk suna bibiya, daga zarar anci nasara kayan sun samu wucewa, kai ba zaka taba sani ba, amma idan aka samu matsala to nan ne za a bibiyi akan wane tikiti kayan suke, sai kaga mutum bai san hawa ba bai san sauka ba, an nuna masa jaka ance tasa ce, alhali shi bai san da ita ba, shi kuma wanda aka sanya yake bibiyar jakar tuni ya cika wandonsa da iska.

Wannan abin yana faruwa a lokacin da kai fasinja ka gama awon kayan da zaka wuce da su, ka shiga wajen da zaka jira zuwan jirgi, sannan ne za a hada baki da su ma'aikata a bude tikitinka a dora maka kayan da ba naka ba, a zahiri ba zaka taba sani ba, har kaje Jeddah in kayan sun shige lafiya ba zaka taba sani ba, amma a kuma kayi awon gaba da kayan da baka sansu ba.

A filin jirgin saman Malam Aminu Kano wannan shi ake kira AWON GABA, asa mutum daukar kayan da bai sansu ba. Wannan kuma yana faruwa ne sakamakon yadda cin hanci ya shiga ko ina, kiri kiri jami'an kula da fasakwauri da NDLEA da sauransu ake hada baki da miyagu daga cikinsu ana safarar abubuwan da basu dace ba.

DUBA WANNAN: An bayar da belin wanda ya saka kwaya a kayan Zainab Aliyu

Abin da mutane da yawa basu sani ba shi ne, da yawan mutane ana goya musu goro a cikin kayansu matukar suna da sarari a tikitinsu, sai anje can, idan ya wuce shi kenan, in kuma bai wuce ba shi daman kawai kayan za a kama ba za'a binciki mai su ba.

Haka nan, yanzu da ake masifar son tafiya da kyawa da hodar iblis, kai fasinja kana zaman zamanka za a jefa ka cikin masifa da bala'i, kamar yadda aka yiwa wannan baiwar Allah Zainab. Muna adduar Allah ya kubutar da ita.

Lallai muna kira ga hukumomin kula da shige da fice na kaya a filin jirgin saman MAKIA da suji tsoron Allah su daina hada baki da miyagun mutane suna sawa matafiya kayan da ba nasu ba a jikin tikitinsu, musamman mukhaddarat da suke da matukar hadari. Allah ka kare matafiyanmu daga wannan sharri, ka tona asirin masu sanyawa mutane kayan da ba nasu ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel