Masu garkuwa da Mutane sun yi awon gaba da Surukin Bafaden Buhari a garin Daura

Masu garkuwa da Mutane sun yi awon gaba da Surukin Bafaden Buhari a garin Daura

Masu ta'addancin garkuwa da Mutane a Yammacin Laraba sun yi awon gaba da Magajin Garin Daura, Musa Umar, yayin da su ka kai farmaki gidan sa da ke garin Daura jim kadan bayan ya gudanar da sallar Maghriba.

Rahotanni kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito sun bayyana cewa, Mallam Umar wanda ya kasance tsohon ma'aikacin hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, ya yi gamo da azal cikin farfajiyar gidan sa na gari Daura a jihar Katsina.

Shugaba Buhari tare da Bafaden sa, Kanal Muhammad Abubakar

Shugaba Buhari tare da Bafaden sa, Kanal Muhammad Abubakar
Source: Twitter

Majaiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, basaraken na gargajiya ya kasance Mahaifi ga Hajiya Fatima Musa, uwargida ga babban bafaden shugaban kasa Muhammad Buhari, Kanal Muhammad Abubakar.

KARANTA KUMA: Firai Ministan Birtaniya ta sallami Ministan tsaro

Mashaida wannan mugun ji da mugun gani sun bayyana cewa, lamari ya auku yayin da maharan rike da bindigu suka rika harbe-harben iska domin tarwatsa al'umma tare da samun damar cin karen su ba bu babbaka.

Bayan sharar hanya ta tabbatar da ingancin gudanar da wannan danyen aiki, masu ta'adar sun yi awon gaba da Magajin Garin Daura cikin wata mota kirar Peugeot 406.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel