Ko Sata kake ko Fashi, Ubangiji zai taimakeka - Dan sanda mai neman cin hanci hannun wani matashi

Ko Sata kake ko Fashi, Ubangiji zai taimakeka - Dan sanda mai neman cin hanci hannun wani matashi

A kokarin da yake na kwatar N,4000 daga hannun mutanen da zai zalunta, dansandan yace: “Ko kana satar motoci ko kai dan Fashi ne, Ubangiji na taimakonka, ku kara kudin su zama N4,000 don mu hudu muke.

An kama wani dansandan Najeriya a hoton bidiyo yana fadin Ubangiji na goyon bayan masu satar motoci da barayi.

Wani mutum mai amfani da kafar sadarwar Twitter mai suna Kayode Ogundamisi ne ya aika da sakon hoton bidiyon da ya zagaye kafofin sadarwar yanar gizo a safiyar Larba.

Kafar labaran SaharaReporters ba ta iya bada lokacin da dansandan ya nemi karbar cin hanci ga mutanen ko wurin da abun ya faru ba.

KU KARANTA: Wasu abubuwa guda shida da Osinbajo ba zai iya yi ba idan shugaba Buhari baya nan

A kokarin kwatar N,4000 daga hannun mutanen da zai zalunta, dansandan yace: “Ko kana satar motoci ko kai dan fashi ne, Ubangiji na taimakonka, ku kara kudin su zama N4,000 don mu hudu muke

Tun farko dai ana iya jin direban motar na cewa: “Ko kasan ko nawa kuka karba daga hannuna yau?”

Kuma dansandan ya amsa da cewa: “Ai kai babban mutum ne."

"Ji mana, Ko kana satar motoci ko kai dan fashi ne, Ubangiji na taimakonka. Na gamsu da hakan. Ku kara kudin su zama N4,000 don mu hudu muke”

Alokacin da aka ba dansandan kudin sai yace: "Nagode. "

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng\

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel