Ranar ma'aikata: NLC ta bukaci El-Rufa'i ya mayar da ma'aikatan da ya kora daga aiki

Ranar ma'aikata: NLC ta bukaci El-Rufa'i ya mayar da ma'aikatan da ya kora daga aiki

Shugaban kungiyar kungiyar kwadago (NLC) reshen jihar Kaduna, Kwamred Ayuba Magaji, ya yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da ya sake waiwayar batun ma'aikatan da ya kora domin mayar da wadanda zasu moru daga cikinsu bakin aiki.

Da yake gabatar da jawabi a filin wasa na 'Ranchers Bees' dake Kaduna yayin bikin ranar ma'aikata na ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, 2019, Kwamred Magaji ya yi kira ga gwamnan da ya gaggauta biyan ma'aikatan da ba za a iya mayar da su ba hakkinsu.

"Ya zama tilas mu yi wannan kira saboda irin halin matsin tattalin arziki da ma'aikatan suka shiga tun baya korar su, wasu ma sun mutu saboda rashin kudin da zasu kula da lafiyar su," a cewar Magaji.

Ranar ma'aikata: NLC ta bukaci El-Rufa'i ya mayar da ma'aikatan da ya kora daga aiki

Nasir El-Rufa'i
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewar zasu duba yiwuwar matsa wa gwamnonin arewa a kan maganar tayar da kamfanin jaridar 'New Nigeria Newspaper' saboda muhimmancin da take da shi ga arewa da kuma kasa bakidaya.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi alhinin mutuwar Hajiya Amina Omoti

A ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun aiki domin shiga sahun ragowar kasashen duniya domin bikin ranar ma'aikata ta duniya.

Kungiyoyin kwadago da gwamnatocin jihohi kan gudanar da taro domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi aiki da kuma hakkin ma'aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel