Wasu abubuwa guda shida da Osinbajo ba zai iya yi ba idan shugaba Buhari baya nan

Wasu abubuwa guda shida da Osinbajo ba zai iya yi ba idan shugaba Buhari baya nan

Akwai jerin wasu abubuwa guda shida da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ba zai iya ba kasar nan har sai ya jira shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da kansa, hakan shine yadda dokar kasar Najeriya ta tsara

A karo na farko kenan tun lokacin da ya zama shugaban kasa, Buhari ya ki sanar da 'yan Najeriya dalilin zuwan shi ziyara kasar Birtaniya, kuma ya ki rubuta wasika ga majalisar dokoki kasar domin sanar da su tafiyar ta sa, sannan kuma ya ki bayyana mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mai rikon kwarya.

Abinda shugaban kasar ya yi ya haifar da kace-nace a kasar, inda kundin tsarin mulki ya bayyana cewa a duk lokacin da shugaban kasa zai tafi hutu ko kuma wani abu makamancin haka, dole ne ya rubuta takarda zuwa ga majalisar dokoki ya bayyana musu halin da ake ciki, sannan kuma ya bayyana musu cewa ya bai wa mataimakin sa rikon kwaryar shugabancin kasar.

Ko da yake mataimakin shugaban kasa na iya taka muhimmiyar rawa wajen kafa manufofi masu amfani a duk lokacin da shugaban kasa bayanan, sai dai kuma ba dukannin abubuwan da shugaban kasa yake yi mataimakinsa zai iya yi ba.

Wasu abubuwa guda shida da Osinbajo ba zai iya yi ba idan shugaba Buhari baya nan

Wasu abubuwa guda shida da Osinbajo ba zai iya yi ba idan shugaba Buhari baya nan
Source: Facebook

Wadanne irin abubuwa ne da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ba zai iya yi ba idan shugaba Buhari bayanan?

  • Ba da mukami babba a gwamnati: Mataimakin shugaban kasa ba zai iya bayar da babban mukami a gwamnati ba, saboda shugaban kasa ne kawai yake da wannan ikon na bai wa wani mukami a gwamnati.
  • Cire wani daga babban mukami na gwamnati: Za a iya tuna cewa Osinbajo ya kori Lawal Daura, a watan Agustan shekarar 2018, lokacin da Buhari yaje birnin Landan hutu. Osinbajo ya yi hakanne saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi shugabancin kasa na rikon kwarya a lokacin, amma yanzu da bai ba shi ba bai da wannan ikon na cire wani daga mukami.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi

  • Sanya hannu akan dokar kasa: A ranar 12 ga watan Yuni, 2017, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2017. Buhari wanda lokacin yana kasar waje yana ganin likita na tsawon kwanaki 40, ya bai wa mataimakin nashi ikon yayi aiki a maimakonsa. Yanzu kuwa da majalisar dokoki ta gabatar da kasafin, dole sai 'yan Najeriya sun jira dawowar shugaban kasa mako mai zuwa domin ya sanya hannu akan kasafin kudin.
  • Umartar hukumomin tsaro: Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ba shi da ikon umartar hukumomin tsaron kasar nan akan wani abu tunda shugaban kasa bai danka mishi kasar a hannunshi ba lokacin da zai yi tafiya.
  • Umartar majalisar dokoki: Ba kamar kasar Amurka ba wacce mataimakin shugaban kasa shi ne shugaban majalisar dattijai, mataimakin shugaban kasa a Najeriya ba shi da wata alaka da majalisar dokoki, sai dai har idan an bashi rikon kwarya.
  • Saka dokan ta baci: Sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana cewa shugaban kasa ne kawai zai iya bayyana dokar ta baci a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel