Wasu sun nuna rashin jin dadinsu da gwamnati ta karbo Zainab Aliyu

Wasu sun nuna rashin jin dadinsu da gwamnati ta karbo Zainab Aliyu

- Mutane da yawa sun nuna rashin jin dadinsu da gwamnati ta sanya baki wurin karbo Zainab Aliyu daga hannun hukumar tsaron kasar Saudiyya

- Sun bayyana cewa tabbas Zainab ta na da laifi, tunda dama dukkanin 'yan matan arewacin Najeriya an riga an yi shaidar su wurin shaye-shaye miyagun kwayoyi

Jim kadan bayan an ceto Zainab Aliyu daga hannun hukumar tsaron kasar Saudiyya, wacce hukumar kasar ke zargin kamata da miyagun kwayoyi, sai aka dinga samun kace-nace a shafin sada zumunta na Twitter, inda wasu ke ganin Zainab na da laifi, saboda babu yadda za ayi wani ya saka mata kwaya a cikin jakarta, musamman da yake ita din ta fito daga yankin arewacin Najeriya ne, wurin da shan kwayoyi ya zama tamkar ruwan dare.

Wasu sun nuna rashin jin dadinsu da gwamnati ta karbo Zainab Aliyu

Wasu sun nuna rashin jin dadinsu da gwamnati ta karbo Zainab Aliyu
Source: UGC

Zainab, wacce take daliba a jami'ar Maitama Sule dake Kano, ta tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano, zuwa kasar Saudiyya, inda aka kamata a kasar Saudiyya da laifin tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Mahaifin Zainab, Habib Aliyu, ya roki gwamnatin Najeriya akan a taimaka a ceto 'yar tashi, nan take shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wasu manya daga cikin ministocinsa akan su ceto Zainab din.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi

Daga baya an sako ta, bayan an bayyana cewa an saka mata kwayar ne a cikin jakarta.

Hakan ne ya sanya 'yan Najeriya yabawa gwamnatin Najeriya da irin namijin kokarin da ta yi wurin ceto rayuwar Zainab. Sai dai kuma wasu sun nuna cewa Zainab na da laifi, kamar yadda kasar Saudiyyar tayi zargi a farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel