Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan

Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan

- Masu garkuwa da mutane sun bayyana dalilan da ya sa suke kama mutane a fadin kasar nan, inda suka dora alhakin abubuwan da suke yi akan gwamnatin Najeriya

- Sun kuma bayyana cewa babu wata hukumar tsaro a kasar nan da ta isa ta hana su abinda suke

Gagararrun masu garkuwa da mutanen nan, wadanda suka kware wurin satar mutane akan babbar hanyar jihar Rivers, sun bayyana dalilan da yasa suka shiga sana'ar garkuwa da mutane.

A kwanakin baya akwai rahotannin da LEGIT.NG ta kawo muku da ke nuni da irin yadda ake satar mutane akan babbar hanyar jihar Rivers din, daya daga cikin wadanda aka kama Mista Happy, wanda aka kama tare da wasu mutane tara a cikin wata motar haya, ranar 25 ga watan Afrilun nan da ya gabata, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Rivers din daga garin Warri.

Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan

Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan
Source: Depositphotos

A cewar Mista Happy, masu garkuwa da mutanen sun sanar da su dalilan da ya sa suke satar mutane, inda suka ce suna yi ne saboda gwamnatin tarayya ta tsaya da biyansu kudin kashewa da take basu duk wata.

KU KARANTA: Bakin ciki ya saka wata tsaleliyar daliba ta kashe kanta

Shirin biyansu kudin wanda tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar'adua, ya bayyana cewa duk 'yan bindigar dake yankin da suka ajiye makamansu, gwamnati za ta dinga biyansu N65,000 duk wata. 'Yan bindigar sun koka kan cewa gwamnati ta dakatar da biyansu kudin, saboda haka dole ne su nemi hanyar da zasu samu abinda za su dinga ci, shine suka yanke shawarar fara wannan sana'ar.

A karshe Mista Happy ya bayyana cewa 'yan bindigar sun bayyana cewa babu wata hukumar tsaron da ta isa ta hana su satar mutane a fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel