Buhari ya yi alhinin mutuwar Hajiya Amina Omoti

Buhari ya yi alhinin mutuwar Hajiya Amina Omoti

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziyya ga iyalin Omoti bisa rasuwar Hajiya Amina Omoti, tsohuwar shugabar (Amirah) kungiyar mata musulmi na Najeriya (FOMWAN).

Sakon ta'aziyyar shugaba Buhari na kunshe ne cikin wani jawabi da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Laraba a Abuja, shugabankasar ya jajanta wa gwamnati da jama'ar jihar Edo da kuma kwamitin koli na kungiyar harkokin addinin Islama bisa rashin marigayiyar.

Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya na musamman ga kungiyar FOMWAN da ma kafatanin al'ummar musulmin Najeriya bisa rashin matar da ya kira 'uwa ta gari, malama kuma shugaba abar kwaikwayo'.

Buhari ya yi alhinin mutuwar Hajiya Amina Omoti

Buhari
Source: Facebook

A cewar sa, za a cigaba da tuna Hajiya Amina a kan gudunmawar da ta bayar wajen yada addinin ba tare da nuna kiyayya ba da kuma mutunta mabiya sauran addinai dake kasar nan.

DUBA WANNAN: An kashe mutum 3, shanu fiye da 300 a sabon rikici a jihar Filato

Ya kara da cewa marigayiyar tayi kokari matuka wajen hada kan mata da tabbtar da cigabansu a lokacin da take shugabacin kungiyar FOMWAN.

A karshe, ya yi addu'ar Allah ya ji kanta, ya sa aiyukanta na alheri su zame mata garkuwa, ya kuma bawa 'yan uwa da abokanta na arziki hakurin jure rashin ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel