Zagon kasa: Jam'iyyar APC reshen jihar Ekiti ta dakatar da tsohon gwamnan jihar

Zagon kasa: Jam'iyyar APC reshen jihar Ekiti ta dakatar da tsohon gwamnan jihar

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ekiti ta dakatar da tsohon gwamna Segun Oni daga jam'iyyar bisa zarginsa da yiwa jam'iyyar zagon kasa.

Vanguard ta ruwaito cewa jam'iyyar ta sanar da dakatar da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar (reshen kudu) ne a cikin wata wasika da aka aike a ranar 1 ga watan Mayun 2019 zuwa ga gwamnan jihar.

A cewar rahoton, jam'iyyar ta APC ta dauki wannan matakin ne bayan Oni ya ki amsa gayyatar da mahukunta jam'iyyar na mazabarsa suka yi masa domin ya wanke kansa daga zargin yiwa jam'iyya zagon kasa da ake masa.

Da duminsa: An dakatar da tsohon mataimakin jam'iyyar APC na kasa

Da duminsa: An dakatar da tsohon mataimakin jam'iyyar APC na kasa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Tsaro: Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni - IG

Wasikar na dauke da sa hannun Shugaba da sakataren jam'iyyar na mazabar Ifaki II, Shina Akinloye da Ogunyemi Taiwo da wasu manyan jami'an jam'iyyar 24 a mazabar.

Wasikar ta ce: "Kamar yadda ya ke sashi na 21 sakin layi na I, II da X na kundin tsarin mulkin APC, mu shugabanin jam'iyyar APC mun dakatar da kai daga jam'iyyar mu mai girma saboda rashin amsa gayyatar da mu kayi maka domin ka kare kan ka daga zargin yiwa jam'iyya zagon kasa da wasu 'yan jam'iyya suka ce ka aikata.

"Za mu aika kofin wannan wasikar ga kwamitocin gudanarwa na karamar hukuma da jiha na jam'iyyar mu domin su dauki matakin da ya dace"

Jaridar ta Vanguard ta ruwaito cewa jam'iyyar ta aike da wasikar gayyata ga Oni a ranar Laraba 24 ga watan Afrilun 2019 domin ya bayyana a gaban kwamitin bincike.

Sai dai Oni ya ki amsa gayyatar da aka yi masa da wani Segun Adetunji ya karba a madadinsa a ranar Alhamis 25 ga watan Afrilun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel