FAAN ta rufe filayen sauka da tashin jirage na jihohin Gombe da Kebbi saboda bashi

FAAN ta rufe filayen sauka da tashin jirage na jihohin Gombe da Kebbi saboda bashi

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na Najeriya (FAAN) ta rufe filayen sauka da tashin jirage na jihohin Gombe da Kebbi saboda bashi da ake binsu da ya haura Naira Miliyan 800.

Rufe filayen sauka da tashin jiragen zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayun 2019.

A sanarwar da FAAN ta aikewa NOTAM na filayen jiragen biyu ta ce za ta janye jami'an kiyaye gobara da ke aiki a filayen jiragen saman da kuma masu gadi da tsaro a filayen jiragen saman.

Bashi: FAAN ta rufe filayen sauka da tashin jirage na jihohin Gombe da Kebbi

Bashi: FAAN ta rufe filayen sauka da tashin jirage na jihohin Gombe da Kebbi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Tsaro: Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni - IG

Tun makonni biyu da suka gabata ne FAAN ta aike da sakon gargadi ga gwamnatocin jihohin biyu amma suka gaza biyan basusukan da ake bin su.

Binciken da jaridar The Nation ta gudanar ya nuna cewa FAAN ta bawa gwamnatocin jihohin isashen lokaci domin su biya basusukan amma suka ki aikata hakan.

An gano cewa hukumar ta FAAN za ta cigaba da bibiyar sauran filayen sauka da tashin jirage na wasu jihohin da ake bin su bashi bayan ta rufe na jihohin Gombe da Kebbi.

An kuma gano cewa FAAN tayi shirin rufe wasu filayen sauka da tashin jirage a wasu jihohin amma wasu daga fadar shugaban kasa suka taka mata birke sai dai duk da hakan ta ce za ta cigaba da rufe dukkan filayen tashin jirage da suke bi bashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel