An kashe mutum 3 da shanu fiye da 300 a sabon rikici a jihar Filato

An kashe mutum 3 da shanu fiye da 300 a sabon rikici a jihar Filato

Rundunar 'yan sanda a Filato ta tabbatar da mutuwar mutum guda da kuma shanu fiye da 300 a sabon rikicin da ya barke a karamar hukumar Bassa dake jihar.

Lamarin ya faru ne bayan wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai hari a kauyen Maiyanga dake masarautar Miango a karamar hukumar Bassa da misalin karfe 8:00 na yammacin ranar Litinin.

A wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, DSP Terna Tyopev, ya fitar ranar Laraba, rundunar ta ce: "hedikwatar rundunar 'yan sanda a jihar Filato ta samu labarin wani hari da wasu 'yan bindiga da ba a san su ba suka kai kauyen Maiyanga dake masarautar Miango da misalin karfe 8:00 na yammacin ranar 29 ga watan Afrilu, 2019, wanda a sakamakon kai harin, wata mata mai suna Jummai Jah, mai shekaru 25, da wani namiji mai suna Emmanuel Ishaya, mai shekaru 37, sun rasa ran su.

"Kazalika, wata jaririya 'yar wata 7 ta samu mummunan rauni a wuya kuma tana karbar magani da samun kula wa a asibitin Enos dake Miango".

An kashe mutum 3 da shanu fiye da 300 a sabon rikici a jihar Filato

Jami'an 'yan sanda
Source: Depositphotos

Rundunar ta cigaba da cewa: "bayanan da muka samu sun nuna cewar an harbe wani mutum, Monday Audu, sannan an daddatsa shi a kauyen Rotsu a masarautar Miango.

"A yayin da muke gudanar da bincike a kan wannan lamari, sai muka samu labari a ranar 30/04/2019 cewar an kai wani hari a kan garken shanu har an kashe 319 tare da raunata wasu 12 da kuma yin awon gaba da wasu 11.

DUBA WANNAN: An bayar da belin wanda ya saka kwaya a kayan Zainab Aliyu

"An nemi wasu makiyaya guda biyu; Mubarak Yakubu da Shehu Saidu, an rasa bayan an kai harin. An kai harin ne a kauyukan Billi da Ariri dake masarautar Miango."

Rundunar ta kara da cewa ta baza jami'anta domin neman makiyayan tare da bin sahun 'yan bindigar domin tabbatar da sun shiga hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel