Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi

Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi

- A karo na biyu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake magana akansabon albashin ma'aikatan Najeriya

- Ya ce babu gudu ba ja da baya gwamnatinsa sai ta biya sabon albashin ga kowanne ma'aikaci a kasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta na nan akan bakan ta na fara biyan ma'aikata sabon albashin da ya sanya hannu a watan Afrilun da ya gabata.

Shugaban kasar ya amince da sanya hannu akan dokar sabon albashin a watan Afrilun da ya gabata. A bisa dokar da shugaban kasar ya sanyawa hannun, za ta bai wa ma'aikatan Najeriya damar daukar albashin N30,000, daga tsohon albashin N18,000 da suke dauka a da.

Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi

Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi
Source: Facebook

Shugaban kasar wanda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilce shi a wurin taron ranar ma'aikata da aka gabatar a filin wasa na Eagle Square dake babban birnin tarayya Abuja, ya tabbatar wa da ma'aikatan kasar nan cewa gwamnati za ta biya sabon albashin da ta sanar cewa za ta fara biya.

Ya kuma tabbatar wa da ma'aikatan cewa gwamnatinsa za ta cigaba da samar da ingantaccen yanayi ga daukacin ma'aikatan kasar nan.

KU KARANTA: Amarya ta haihu a daidai lokacin da ake daura mata aure

A lokacin da yake bayani, ya bayyana cewa, "Ya kamata mu ajiye siyasa da bambancin akida a gefe mu hada kai wurin kawo cigaba mai dorewa a kasar nan."

Ya ce za su mai da hankali wurin gyara wutar lantarki a kasar nan, wurin samar da ingantattun kayan aiki masu dorewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel