Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto

Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto

-Ma'aikata kalilan ne suka halarci taron ranar ma'aikata a Sokoto

-Ma'aikatan jihar Sokoto suna rokon gwamnatin jihar da ta fara biyan sabon mafi karancin albashin N30,000

Bikin ranar ma’aikata na wannan shekara a jihar Sokoto bai yi armashi ba saboda da dama daga cikin ma’aikata basu halarci taron ba.

Kadan daga cikin ma’aikatan da suka halarci wannan taro da akayi a filin kwallon Giginya dake jihar, sun shaidawa manema labarai cewa hakan ya biyo bayan rashin biyan albashin watan Afirilu da ba’ayi ba.

Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto

Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto
Source: Twitter

KARANTA WANNAN:Buhari ya jinjinama masu yiwa kasa hidima saboda jajircewarsu

“ Wasunmu basu da kudi da zasu kawo kansu wannan wajen” a cewar daya daga cikin ma’aikatan dake wurin.

A jawabinsa kuwa shugaban kungiyar kwadago ta kasa wato NLC reshen jihar Sokoto, Kwamarad Aminu Umar ya roki gwamnatin jihar da ta soma biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000.

Ya kuma sake rokonta da ta duba al’amarin malaman makarantar da suka ajiye aiki da kuma ma’aikatan kananan hukumomi domin a biyasu hakkinsu.

Shugaban ya nemi gwamnati da ta biya malaman makarantun firamare da sakandaren jihar bashin da suke bi na albashi sannan kuma da kudin makarantun gaba da sakantare na zuwa hutun karshen shekarar 2018.

Gwamna Tambuwal wanda shugaban ma’aikata na jihar ya wakilta Dr Buhari Bello Kware yace, hakika gwamnati tayi matukar kokari a bangaren jindadin ma’aikatan jihar.

Bugu da kari, ya kara da cewa daga cikin bukatun ma’aikatan gwamnati zatayi iya bakin kokarinta domin sama masu walwala da jindadi har ma da kara horar da su akan ayyukansu, ganin cewa jindadin ma’aikata yana daga cikin manyan manufofin gwamnatinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel