Ganduje ya yi alkawarin fara biyan ma'aikatan Kano sabuwar albashi

Ganduje ya yi alkawarin fara biyan ma'aikatan Kano sabuwar albashi

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin fara biyan sabon karin albashi na N30,000 ga ma'aikatar jiharsa.

Ya yi wannan alkawarin ne a ranar Laraba a wurin bikin ranar ma'aikata na kasa da aka gudanar a Sani Abacha Stadium da Kano a babban birnin Jihar.

A yayin da ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta cigaba da aiki lafiya tare da ma'aikata, ya kuma ce gwamnatinsa za ta cigaba da bayar da horo ga ma'aikata a jihar.

Ganduje ya yi alkawarin fara biyan sabuwar albashi

Ganduje ya yi alkawarin fara biyan sabuwar albashi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Tsaro: Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni - IG

"Abin farko da muke tsamani shine kaddamar da biyan sabon albashi saboda muhimmancin sa a gare mu.

"Kuma, akwai batun horo sake bawa ma'aikata horo da kuma karin girma. Za mu mayar da hankali sosai a kan wadannan batutuwan saboda suna da muhimmanci a gare mu," inji shi.

Ganduje ya yabawa ma'aikata kasar nan tare da jadada muhimmancin zamantakewa mai kyau tsakanin ma'aikata da wadanda suka dauke su aiki.

A bangarensa, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ware muhimman abubuwa da za a gudanar domin karrama ma'aikata a jihar.

A cewarsa, gwamnatinsa ta shirya wata liyafa da za a gudanar domin karrama ma'aikata da masu daukan aiki da suka nuna kwazo da bajinta wurin gudanar da ayyukansu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel