Yanzu Yanzu: Ma'aikata sun nuna kin amincewarsu a kan karin farashin man fetur da haraji

Yanzu Yanzu: Ma'aikata sun nuna kin amincewarsu a kan karin farashin man fetur da haraji

Hadadaiyar kungiyar Kwadago ta ce ba za ta amince da karin kudin man fetur da harajin kayayakin masarafi na VAT a yayin da suke kira ga gwamnati tayi garambawul ga tsarin tsaro na kasar.

A jawabin da kungiyar tayi a ranar 1 ga watan Mayu wurin bikin ranar ma'aikata da aka gudanar da Eagle Square a Abuja, ta ce karin kudin man fetur da VAT zai kara radadin talauci da ake fama da shi a kasar.

Shugaban kungiyar Kwadago na Najeriya, (NLC) Ayuba Wabba da shugaban Kungiyoyin 'yan kasuwa, (TUC), Bobboi Bala Kaigama ne suka karanto jawabin ga dubban ma'aikata da suka hallarci taron.

Yanzu Yanzu: Ma'aikata sun nuna kin amincewarsu a kan karin farashin man fetur da haraji

Yanzu Yanzu: Ma'aikata sun nuna kin amincewarsu a kan karin farashin man fetur da haraji
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

"Kungiyar Kwadago tana juyayin yadda ake samun layin ababen hawa a gidajen mai a biranen mu. Munyi imanin hakan ya faru ne saboda shawarar da asusun bayar da lamuni, IMF ta bawa gwamnatin mu na cewa ta janye tallafin man fetur.

"Abinda IMF ke nufi da janye tallafin man fetur shine karin kudin man fetur da karin walhalun rayuwa.

"Ma'aikatan Najeriya sun gano cewa abubuwa uku ne IMF ke damun Najeriya a kai - Janye tallafin man fetur, karya darajar Naira da kuma bude iyakan kasashen mu domin a rika shigo da kayayakin kasashen waje," inji ma'aikatan.

Ma'aikatan sunyi kira da shugabanin siyasa su mayar da hankulansu wurin yiwa al'umma aiki da kuma tausayawa al'ummar Najeriya saboda irin wahalhalun rayuwa da suke fama da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel