An bayar da belin wanda ya saka kwaya a kayan Zainab Aliyu

An bayar da belin wanda ya saka kwaya a kayan Zainab Aliyu

Abike Dabiri-Erewa, mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren harkokin kasashen waje, ta sanar da cewar an bayar da belin mutumin da aka zargi da saka kwayar tramol a jakar kayan matashiyar nan Zainab Aliyu da kadan ya rage hukumomin kasar Saudiyya ta aika ta lahira bisa zarginta da safarar kwa zuwa kasar Saudiyya.

A ranar Talata ne hukumomin Saudiyya suka saki Zainab bayan ta shafe kusan watanni 6 a gidan yarin kasar bayan an kama ta bisa zargin ta shiga da kwaya kasar saudiyya.

A jawabin da babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ya fitar, ya ce yanzu haka Zainab na ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Saudiyya.

Kazalika, ya bayyana cewa hukumomin kasar Saudiyya za su saki Ibrahim Abubakar, wani dan Najeriya da ya samu irin matsalar Zainab a kasar Saudiyya.

An bayar da belin wanda ya saka kwaya a kayan Zainab Aliyu

Zainab Aliyu
Source: Twitter

Sai dai, Dabiri-Erewa ba ta bayar da cikakken bayani a kan mutumin da aka bayar belin ba, kazalika ba ta bayyana a wacce kotu ne aka gurfanar da shi ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama wanda ya sace shugaban UBEC da diyarsa a hanyar Abuja

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama Zainab, daliba a jami'ar Maitama Sule dake Kano, a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2018 bisa zarginta da shiga da jaka dauke da kwayar 'tramol' zuwa kasar Saudiyya.

Matashiyar ta tashi zuwa kasar Sauddiya daga filin jirgin sama na Mallam Aminu domin gudanar da aikin 'umra' tare da mahaifiyarta, Maryam, da 'yar uwarta, Hajara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel