Martanin Shugaba Buhari ga Atiku: Ban bada kwangilar buga takardun zabe ba ga dan jam'iyyar APC

Martanin Shugaba Buhari ga Atiku: Ban bada kwangilar buga takardun zabe ba ga dan jam'iyyar APC

- Ana cigaba da fafatawa tsakanin lauyoyin shugaba Buhari da na Atiku a kotun zabe

- Atiku da jam'iyyar PDP sun zargin cewa Buhari ya bayar da kwangilan buga kayan aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karyata zargin bayar da kwangilar buga kayan zaben shugaban kasa da a aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairun 2019, ga wani dan jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PDP da dan takarar shugabancin kasar ta, Atiku Abubakar, a daya daga cikin hujjojin da suka kafa cikin korafin da suka gabatar ga Kotun Sauraron Kararrakin Zabe a Kotun Daukaka Kara dake Abuja, sunyi ikirarin cewa zaben da aka gudanar tattare yake da ayukkan cin hanci, wanda daya daga cikin su shine bada kwangilar buga Katunan Zabe (PVC) ga wani kamfani da ake kira Activate Technologies Limited, mallakar Alhaji Mohammed Musa, wani dan takarar kujerar Sanata a jihar Neja.

Amma a wani martanin da shugaban kasar yayi ta hanyar wata tawagar lauyoyi a karkashin jagorancin Wole Olanipekun (SAN), yace Alhaji Mohammed ba dan jam’iyyar APC ba ne, inda ya kara da cewa ba wata kwangilar da aka ba shi, kuma sunan “Activate Technologies da aka ambata a cikin sakin layi na 356 na takardar korafin ba mutum daya ba ne da Alhaji Mohammed Musa.”

KU KARANTA: Ranar ma’aikata: Ma’aikata kadan ne suka halarci taron wannan rana a Sokoto

Shugaban kasar ya kara da cewa anba kamfanin kwangilar aikin ne a shekara 2011, ba wai “a lokacin zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 ba, kamar yadda aka yi zargi kan kuskure.

“Buga katunan zabe da kamfanin Activate Technologies Yayi ba zai iya kuma bai shafi zaben ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 ba ta kowace hanya, don ana amfani da bin tsarin wasu lambobi ne da kuma bayanan masu mallakar katunan zaben, kuma kati daya ne kawai za iya ba mutum bayan an tantance shi.

Shugaban kasa kuma yace sabanin ikirarin da jam’iyyar PDP tayi, babu wani zumunci na jini a tsakanin sa da Jami’ar Hukumar Zabe ta kasa, Malama Amina Zakari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel