APC ta karbe kaf Majalisar dokokin Jihar Legas bayan Olarunrinu ya bar PDP

APC ta karbe kaf Majalisar dokokin Jihar Legas bayan Olarunrinu ya bar PDP

Mun samu labari cewa Dapo Olorunrinu, wanda shi kadai ne ‘dan jam’iyyar PDP mai adawa a cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Legas, ya sauya-sheka a halin yanzu zuwa APC mai mulki.

Ficewar Rt. Hon. Dapo Olarunrinu daga jam’iyyar adawa ta PDP yana nufin cewa yanzu PDP ba ta da ‘dan majalisa ko guda a Legas. Jam’iyyar APC mai mulki ta samu cikakken iko da majalisar dokokin Legas din ne bayan zaben 2019.

Kawo yanzu Dapo Olorunrinu mai wakiltar Mazabar Amuwo-Odofin na jihar Legas wanda ya sha kasa a zaben 2019 shi kadai ne ke rike da tutar PDP, shi ma dai yayi maza yanzu ya bi sahun sauran Abokan aikin sa ya koma tafiyar APC.

KU KARANTA: Jam’iyyar APGA ta shiga hargitsi bayan ta rasa 'Dan Majalisa

APC ta karbe kaf Majalisar dokokin Jihar Legas bayan Olarunrinu ya bar PDP

PDP ta rasa ‘Yan majalisan ta 8 a Legas a shekaru Legas
Source: UGC

A Ranar Litinin, 29 ga Watan Afrilu ne Dapo Olorunrinu, ya fadawa ‘yan majalisar dokokin na Legas cewa ya fice daga PDP ya dawo APC, Azeez Sanni, shi ne wanda ya karanta wasikar da aka aikowa Kakakin majalisar dokokin jihar.

Olorunrinu ya godewa shugaban majalisa, Mudashiru Obasa, da irin kokarin da yayi masa a yankinsa duk da banbancin jam’iyyar da ke tsakaninsu a lokacin. Olarurinu yace ya zama dole ya koma APC mai neman ganin cigaban kasar.

Dapo Olorunrinu ya sha kashi ne a hannun ‘dan takarar APC a zaben bana watau Mojisola Alli-Macaulay, inda ya kuma ce ba zai tafi kotu ba duk da cewa da kuri’a 278 rak aka doke sa a zaben da aka yi a cikin Watan Mayun nan da ya wuce.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel