Yan bindiga sun kashe mutum 10 a garuruwan Katsina

Yan bindiga sun kashe mutum 10 a garuruwan Katsina

Rundunan yan sanda reshen jihar Katsina ta tabbatar kisan mutane 10 da yan bindiga suka kashe a kauyukan karamar hukumar Gobirawa da Sabawa dake jihar.

Wannan ya zo ne a jawabin da kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya bayar, a ranar Laraba a Katsina.

Ya bayyana cewa yan bindigan sun zo akan babura akalla 150 misalin karfe 6:10 na yammacin ranar Talata, sannan suka kai hari ga kauyukan biyu.

Isah har ila yau yace yan bindigan sun saci dabbobi tare da kaddarori bayan sun kashe mutanen.

Yan bindiga sun kashe mutum 10 a garuruwan Katsina

Yan bindiga sun kashe mutum 10 a garuruwan Katsina
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa teshen rundunar cikin gaggawa ta tura jami’an yan sanda don gudanar da ayyuka a kauyukan da lamarin ya shafa, sunyi nasaran kora yan bindigan bayan musayar wuta.

KU KARANTA KUMA: Hukumar DPR ta nemi a koyawa direbobin tanka dubarun kashe wuta

A cewar shi, yan sandan suna nan suna kokarin ganin sun kame yan bindigan.

Yace, “Zamu yi iya kokarinmu wajen ganin mun cafke masu hannu cikin wannan mugun aikin, zamu yi adalci sannan kuma zamu kawo karshe ga ayyukan miyagun mutane."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar, na jihar Zamfara ya roki jami’an tsaro da su koma yankunan da yan ta’adda suka addabi mutane a jihar sannan sun yi arangama dasu.

Gwamna Yari yayi rokon ne a wani taron manema labarai jim kadan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki akan tsaro a jihar.

Yari ya nuna damuwa kan halin wasu jami’an tsaro na zama a cikin birane maimakon a kauyukan da yan bindiga suke cin karensu ba babbaka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel