Ikem Uzozie yayi watsi da APGA ya koma APC mai adawa a Anambra

Ikem Uzozie yayi watsi da APGA ya koma APC mai adawa a Anambra

Mun samu labari daga Jaridar Vanguard cewa wani ‘dan majalisar jam’iyyar APGA wanda yake wakiltar Mazabar yankin Aguata II a majalisar dokokin jihar Anambra, ya sauya-sheka zuwa APC.

Rt. Hon. Ikem Uzozie yayi watsi da APGA ne inda ya koma jirgin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya a Ranar Talatar nan 30 ga Watan Afrilu. Honarabul Uzozie ya bayyana sauyin-shekan na sa ne a gaban farfajiyar majalisar dokoki.

Ikem Uzozie ya boye dalilan da su ka sa ya bar APGA ya koma APC, inda yace shi kadai ya san abin da ya sa ya dauki wannan mataki. Kwanaki ne dai Ikem Uzozie ya zama Kakakin ‘Yan taware a majalisar dokokiin jihar Anambra.

KU KARANTA: Buhari zai mamayi APC da mutanensa wajen rabon Ministoci

Ikem Uzozie yayi watsi da APGA ya koma APC mai adawa a Anambra

'Dan MajalisarJam’iyyar APGA ya koma APC a Anambra
Source: Depositphotos

Hakan ya faru ne bayan an yi yunkurin tsige shugaban majalisar jihar, Rita Maduagwu. A halin yanzu Hon. Ike Uzozie yace APGA tana fama da rikicin cikin-gida tun bayan rigimar da ya barke kwanakin baya har ta kai aka dakatar da shi.

‘Dan majalisar ya fadawa ‘yan jarida cewa ya dauki wannan mataki ne bayan jam’iyyar APGA ta shafe watanni 5 ba ta janye dakatarwar da tayi masa ba, duk da cewa yayi ta bin hanyar lalama domin ayi masa afuwa amma abin ya gagara.

Idan an kafa sabuwar majalisa wannan karo, ‘Ya ‘yan jam’iyyar APGA da ke majalisar dokokin za su rage yawa daga kujeru 27 a baya zuwa 24, bayan wasu sun sauya-sheka kwanan nan, sannan kuma PDP ta lashe wasu kujeru a zaben 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel