Wani Jami'in 'Dan Sanda yace Ubangiji ya yarda da sata

Wani Jami'in 'Dan Sanda yace Ubangiji ya yarda da sata

Baya ga harbi da kisan ganganci da suke yi ma yan Najeriya, alamu sun nuna cewa jami’an yan sandan Najeriya sun iya sakin zance marasa amfani kuma na ganganci.

Yan makonni da suka gabata yan Najeriya da dama a shafin zumunta sun tofa albarkacin bakunansu lokacin da wani babban jami’in dan sanda, mataimakin kwamishinan yan sanda kuma Shugaban sashin korafe-korafen jama’a, Yomi Shogunle ya shawarci yan Najeriya akan wani hanyar guje ma katobarar yan sandan Najeriya.

Ya shawarci jama’a da su guje ma yin turancin iyayi ga jami’an maimakon haka suyi masu turancin gwaranci domin a zauna lafiya.

A cewarsa hakan zai kare mutane daga fadama matsalar yan sanda.

Sai dai yan Najeriya sun yi watsi da jawabin Shogunle a matsayin furucin ganganci na nuna rashin cikakken ilimin jami’an yan sandan Najeriya.

Ana haka ne kuma sai ga wani jami’in dan sanda a sabuwar bidiyo yana fadin cewa “ko Ubangiji ya goyi bayan sata” a yaran Yarbanci yayinda yake karban kudi daga hannun masu ababen hawa.

Yayinda mai motar ke korafin cewa ya ba jami’an yan sanda da dama kudi akan hanyarsa ta zuwa, sannan kuma jami’in dan sandan da ba a gano kowanene bay ace shima sai ya bashi naira dubu-dubu guda hudu.

KU KARANTA KUMA: Ku koma filin daga – Yari ga jami’an tsaro

“...Satar ababen hawa, fashi... ko Ubangiji na goyon bayan hakan,” inji dan sandan.

“Dole ka zamar dashi hudu fa. Mu hudu ne. Zaka yi tafiyarka lafiya,” inji dan sandan yayinda yake neman a bashi yar dubu-dubu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel