Oyetola ya shawarci shuwagabannin ma’aikata na yankin kudu maso yamma da suyi kokarin ciyar da yankin gaba

Oyetola ya shawarci shuwagabannin ma’aikata na yankin kudu maso yamma da suyi kokarin ciyar da yankin gaba

- Ku zama tsintsiya madaurinki daya, Oyetola ya shawarci shugabannin ma'aikatan yankin kudu maso yamma

- Oyetola yace akwai aiki ja a gabansu domin ganin sun dawo da martabar yankinsu

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya shawarci shuwagabannin ma’aikata na yankin jihohin kudu maso yamma da suyi aiki domin cigaban yankinsu.

Yace aikin nasu yakamata ya zama suna yin shine da niyyar farfado da martabar yankin nasu wacce suka rasa, ta hanyar amfani da ma’aikata gwamnati dake jihohinsu.

Oyetola ya shawarci shuwagabannin ma’aikata na yankin kudu maso yamma da suyi kokarin ciyar da yankin gaba

Oyetola ya shawarci shuwagabannin ma’aikata na yankin kudu maso yamma da suyi kokarin ciyar da yankin gaba
Source: Twitter

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya ta kashe N3.5trn wurin ayyukan gine-ginen raya kasa a shekara 3, inji Osinbajo

Oyetola ya kara da cewa, a ganinshi hanya daya ce zata iya samar masu da cigaba wanda kowa zai alfahari dashi a yankin. Musamman idan suka tuna da turbar da magabatansu suka daura su akai. Saboda haka sai ma’aikata sun jajirce kwarai da gaske.

Gwamna Oyetola yayi wannan jan hankalin ne ranar Talata wurin bude wani taro na musamman da ya kunshi shuwagabannin ma’aikata na jihohin kudu maso yammancin Najeriya da kuma wasu masu ruwa da tsaki cikin lamarin a babban birnin jihar Osun.

Wadanda suka halarci taron sun hada da: shugabannin ma’aikatan jihohin Osun, Oyo, Ondo, Ogun, Ekiti da kuma Legas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel