Mayakan Boko Haram sun kashe masu yankan itace 14 a dajin Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe masu yankan itace 14 a dajin Borno

Mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram sun kashe wasu mutane goma sha hudu dake sana’ar yakan itatuwa daga dazukan jahar Borno suna sayar ma jama’a a cikin gari don girki, kamar yadda wasu matasan sa kai na ‘Civilian JTF suka bayyana’.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito abokan aikinsu ne suka tsinci gawarwakin mutanen ne a kauyen Duwabayi dake kusa da garin Monguno a daren Talata, 30 ga watan Afrilu, inda daga bisani Yansanda suka kwashe gawarwakin.

KU KARANTA: Ceto Zainab Aliyu: Gwamna Ganduje ya jinjina ma shugaba Muhammadu Buhari

A shekarar data gabata ne kafatanin jama’an kauyen Duwabayi suka tattara inasu inasu suka watse daga kauyen sakamakon yawan hare haren da Boko Haram take kai musu, inda suka koma zama a sansanonin yan gudun hijira dake Monguno.

Wani mazaunin kauyen mai suna Kulo Gana ya bayyana cewa “Yansanda sun kwaso gawarwaki guda goma sha hudu zuwa ofishinsu dake Monguno, kuma jama’a da dama suna ta zuwa ofishin Yansandan don duba fuskokin da zasu iya ganewa a cikinsu.”

Shima wani mazaunin kauyen, Bunami Mukhtar ya bayyana ma majiyarmu cewa duka gawarwakin guda goma sha hudu suna dauke da raunukan alburusai a jikkunansu.

Su dai wadannan mutane 14 suna zaune ne a sansanonin yan gudun hijira, inda mazauna sansanin ke dogaro da abincin da gwamnati ko kungiyoyi masu zaman kansu suka kawo musu don rayuwa, hakan tasa wasu daga cikinsu suka fara sana’ar saran itace suna sayarwa don samun kudin shiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel