An saki mutum 3 da aka yi garkuwa da su a Kajuru – Yan sanda

An saki mutum 3 da aka yi garkuwa da su a Kajuru – Yan sanda

Rundunar yan sanda ta bayyana sakin mutum uku da aka yi garkuwa dasu a Kajuru, karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.

Labarin sakin na kunshe ne a wani jawabi daga Yakubu Sabom jami’in hulda da jamaá na rundunar yan sandan Kaduna a daren ranar Talata, 30 ga watan Afrilu.

Jawabin ya bayyana cewa anyi nasarar sakin nasu ne bayan matsin lambar da yan sanda suka saw a masu garkuwan.

A ranar 19 ga watan Afrilu ne, aka sace mutanen su uku a Kajuru lokacin day an bindiga suka kai hari wajen.

An saki mutum 3 da aka yi garkuwa da su a Kajuru – Yan sanda

An saki mutum 3 da aka yi garkuwa da su a Kajuru – Yan sanda
Source: Depositphotos

Harin yayi sanadiyar mutuwar wata yar kasar Birtaniya, Faye Mooney da wani dan Najeriya Matthew Oguche.

Koda dai yan sanda sunyi alkawarin tabbatar da sakinsu akan lokaci, hakan bai cimma nasara ba sai bayan da suka shafe kwanaki 12 a tsare.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya zata tabbatar masu karamin karfi sun samu kulawa akan lafiyarsu

Ba a bayyana sunayen mutanen uku ba. Sannan jawabin bai kuma bayyana ko an biya kudin fansa kafin sakin nasu ba.

Harin ya janyo hankalin majalisar dattawan Najeriya. Bayan sun yi shiru na minti daya don karrama Ms Mooney, yan majalisan sun aika sammaci ga Shugaban yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, da ya bayyana a gaban majalisar domin ya bayar da jawabi kan kokatin kore laifuka.

Mista Adamu zai gurfana gaban majalisa a ranar 7 ga watan Mayu, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana a ranar Talata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel