Yan sandan Kebbi sun kama mutum 6 kan zambar N19m

Yan sandan Kebbi sun kama mutum 6 kan zambar N19m

Rundunar yan sandan jihar Kebbi sun kama wani mutum mai suna Okafor Lazarus da wasu mutane biyar akan zargin zambar makudan kudi har naira miliyan 19.

A cewar hukumar yan sandan, jami’an SARS na Lagas da jami’an CID daga rundunar Kebbi ne suka kama mutanen su shida kan zargin damfarar wani mai suna Frances Ezeobele kudi naira miliyan 19 a Birnin Kebbi.

Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan yan sanda na jihar, Garba Muhammed Danjuma yace yan sandan sun fara bincike a cikin kamarin sannan za su kai maganar kotu bayan bincikensu.

Yan sandan Kebbi sun kama mutum 6 kan zambar N19m

Yan sandan Kebbi sun kama mutum 6 kan zambar N19m
Source: Depositphotos

Yan sandan sun kuma kama wani mai suna Yakubu Abubakar kan zargin satar mota kirar Toyota Carina II.

Yan sandan sunce a dauke motar ne daga inda aka ajiye ta amma jami’anta sun kama mai laifin a yankin Gwadangwaji da ke Birnin Kebbi.

KU KARANTA KUMA: Ya zama wajibi malamai su mara wa shugabanni baya kan matsalar tsaro – Sheikh Pantami

A wani lamarin kuma, jami’an yan sanda a yankin Yauri da ke jihar Kebbi sun kama wani Aliyu Umar na kauyen Bagu, karamar hukumar New Bussa da ke jihar Niger kan zargin mallakar dalar Amurka 100 har guda tara.

Yace har yanzu ana kan bincike akan lamarin yayinda yan sanda ke jiran tabbaci daga babban bankin Najeriya kan lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel