Ya zama wajibi malamai su mara wa shugabanni baya kan matsalar tsaro – Sheikh Pantami

Ya zama wajibi malamai su mara wa shugabanni baya kan matsalar tsaro – Sheikh Pantami

Biyo bayan tarin matsala na rashin tsaro da tabarbarewar tarbiya da ke hauhawa a kasar Najeriya, an yi kira ga shugabannin addini da su tsaya tsayin daka wajen ganin sun mara wa gwamnatin tarayya baya akan kokarinta na shawo kan matsalolin.

Sheikh Isah Ali Ibrahim Pantami, daya daga cikin manyan malaman addinin musulunci a kasar ne yayi wannan kira a yayinda yake jawabi a taron kara wa juna sani na kwanaki uku da aka gudanar na kungiyar Izala.

An gudanar da taron ne dakin taro na makarantar kimiya na kungiyar da ke a titin Zariya da ke Jos ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce, yawan abubuwan assha da ke faruwa a kasar nan a yanzu irinsu ba ya faruwa shekaru 30 da su ka gabata.

Ya zama wajibi malamai su mara wa shugabanni baya kan matsalar tsaro – Sheikh Pantami

Ya zama wajibi malamai su mara wa shugabanni baya kan matsalar tsaro – Sheikh Pantami
Source: Twitter

Ya furta cewa, shan muggan kwayoyi, kamar su kodin da wadansu ababen sa maye, yawan zinace-zinace da yin luwadi da madigo da aikin ta’addanci, kamar garkuwa da mutane a nemi fansa, da yawan sace-sacen shanu da kashe masu shanun da sace matayensu a yi mu su fyade, abu ne da ya ke ci wa wannan gwamnati tuwo a kwarya.

Dr. Pantami, wanda shi ne darakta janar na hukumar kimiyya ta tarayya ta NITDA kuma babban bako mai jawabi a gurin bikin bitar, ya ce, “ba abinda ya fi damun shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar matsalar rashin tsaro a kasar nan, musamman a jihohin Arewacin kasar.”

Don haka sai ya kara yin kira ga malaman da su kara jajircewa wajen yin wa’azuzzuka a kan abubuwan da Allah (SWT) ya yi haramci a kan aikata su da irin sakamakon masu aikata su za su samu idan su ka mutu ba sa tuba ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya zata tabbatar masu karamin karfi sun samu kulawa akan lafiyarsu

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar, na jihar Zamfara ya roki jami’an tsaro da su koma yankunan da yan ta’adda suka addabi mutane a jihar sannan sun yi arangama dasu.

Gwamna Yari yayi rokon ne a wani taron manema labarai jim kadan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki akan tsaro a jihar.

Yari ya nuna damuwa kan halin wasu jami’an tsaro na zama a cikin birane maimakon a kauyukan da yan bindiga suke cin karensu ba babbaka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel