Ku koma filin daga – Yari ga jami’an tsaro

Ku koma filin daga – Yari ga jami’an tsaro

Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar, na jihar Zamfara ya roki jami’an tsaro da su koma yankunan da yan ta’adda suka addabi mutane a jihar sannan sun yi arangama dasu.

Gwamna Yari yayi rokon ne a wani taron manema labarai jim kadan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki akan tsaro a jihar.

Yari ya nuna damuwa kan halin wasu jami’an tsaro na zama a cikin birane maimakon a kauyukan da yan bindiga suke cin karensu ba babbaka.

Gwamnan ya ba jami’an tsaro tabbacin cewa gwamnatin jihar a shirye take domin tallafa masu da ababen jin dadi da wuraren kwana domin taimaka masu wajen kakkabe yan ta’adda daga jihar.

Ku koma filin daga – Yari ga jami’an tsaro

Ku koma filin daga – Yari ga jami’an tsaro
Source: Twitter

Gwamnan ya kuma yi korafi akan rashin jami’an tsaro a yankunan karkara a jihar wanda yan ta’adda ke kai hari da sace-sace ba tare da an dauki mataki ba.

KU KARANTA KUMA: Ban ba dan APC kwangilar kayayyakin zabe ba – Buhari ga Atiku

Yari yayi maraba da haramta ayyukan hakar ma’adinai a jihar, inda ya bayyana cewa jihar bata samun ko sisi daga ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma nuna yakinin cewa za a dauki mataki domin magance kalubalen tsaro a jihar sannan a dawo da zaman lafiya.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa gwamnatin tarayya wajen kawo zaman lafiya mai dorewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel