Ban ba dan APC kwangilar kayayyakin zabe ba – Buhari ga Atiku

Ban ba dan APC kwangilar kayayyakin zabe ba – Buhari ga Atiku

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karyata zargin ba dan APC kwangilar kayayyakin zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun, 2019.

Jam’iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, a korafin da suka shigar kotun zaben Shugaban kasa a Abuja, sun yi ikirarin cewa anyi magudi a zabe, inda daga ciki suka ce an bai wa kamfanin Activate Technology Limited, wacce ke mallakar Alhaji Mohammed Musa, dan takarar kujerar sanata a APC da ke jihar Niger kwangilar buga katunan zabe.

Amma da yake mayar da martani ta tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Wole Olanipekun (SAN), Shugaban kasar ya bayyana cewa Alhaji Mohammed ba dan APC bane, inda ya kara da cewa kwangilar da aka basa da kamfanin “Activate Technologies Limited da suke ikirari a kararsu ba mutum guda bane da Alhaji Mohammed Musa.”

Ban ba dan APC kwangilar kayayyakin zabe ba – Buhari ga Atiku
Ban ba dan APC kwangilar kayayyakin zabe ba – Buhari ga Atiku
Source: Depositphotos

Shugaban kasar ya i gaba da bayyana cewa an ba kamfanin kwangilar ne tun a 2011 ba wai a yayin dage zaben Shugaban kasa na 23 ga watan Fabrairu, 2019 ba kamar yadda aka yi kuskuren bayyanawa a karar.

KU KARANTA KUMA: Matasan Kogi sun tara N2m domin tazarcen Bello

“Buga katunan zabe da Activate Technologies Ltd. Ba zai shafi kuma bai shafi zaben ranar 23 ga watan Fabraitu ba, ta kowani hali, kamar yadda aka buga katunan zabe daidai adadin wadanda aka yiwa rijista, kuma katin zabe daya aka baiwa kowani mutum guda da yayi rijista bayan tabbatar da asalin mai zaben,” inji shi.

Shugaban kasar ya kuma jadadda cewa sabanin ikirarin PDP, bashi da wata alaka ta jini da jami’ar INEC, Misis Amina Zakari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel