Gungun yan bindiga sun kai farmaki Filato, sun halaka mutum 2

Gungun yan bindiga sun kai farmaki Filato, sun halaka mutum 2

Wasu gungun yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Maiyanga dake cikin yankin Miango na karamar hukumar Bassa ta jahar Filato, inda suka kashe akalla mutane biyu tare da jikkata wani jariri mai watanni bakwai kacal a duniya.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Filato, DSP Terna Tyopev ne ya bayyana haka a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace lamarin ya faru ne a daren Litinin.

KU KARANTA: Ba za muyi murnar sakin Zainab ba har sai Buhari ya kubutar da Leah – kungiyar CAN

“Da daren Litinin muka samu labarin wasu yan bindiga sun kaddamar da hari a kauyan Maiyanga dake cikin lardin Miango na karamar hukumar Bassa, inda suka kashe mutane biyu, Jummai Jah mai shekaru 25 da Emmanuel Ishaya mai shekaru 37.

“Haka zalika sun jikkata wata jaririyar yar wata 7, mai suna Tabitha a yayin harin, inda suka sareta da adda a wuya, amma a yanzu haka tana samun kulawa a Asibitin Enos dake garin Mangu.” Inji shi.

Bugu da kari, Kaakakin yace wasu yan bindiga sun kai ma shanu 319 hari a ranar Talata, inda suka kashe shanu 12, sa’annan suka yi awon gaba da wasu shanu 11 a kauyukan Billi da Ariri cikin lardin Miango, sa’annan an nemi yaran dake kiwonsu su biyu, Mubarak Yakubu da Shehu Saidu an rasa.

Dansanda Terna yace rundunar Yansandan jahar ta tura karin jami’an tsaro zuwa yankin domin gano yaran biyu, tare da kokarin gano duk masu hannu cikin harin da kuma kamasu domin su fuskanci hukuncin abinda suka aikata.

Daga karshe DSP Terna ya nemi jama’a su rungumi zaman lafiya da juna, tare da yin biyayya ga doka da oda domin samun dawwamammen zaman lafiya, sa’annan yace Yansanda zasu cigaba da kokarin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyan al’umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel