Ceto Zainab Aliyu: Gwamna Ganduje ya jinjina ma shugaba Muhammadu Buhari

Ceto Zainab Aliyu: Gwamna Ganduje ya jinjina ma shugaba Muhammadu Buhari

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya jinjina tare da mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa namijin kokarin da tayi wajen ceto Zainab Aliyu, yarinyar da ake zargi da safarar kwarar zuwa kasar Saudiyya.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Malam Mohammed Garba ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu inda yace gwamnati tayi kokari matuka ta yadda ta gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar Zainab.

KU KARANTA: Ba za muyi murnar sakin Zainab ba har sai Buhari ya kubutar da Leah – kungiyar CAN

Ceto Zainab Aliyu: Gwamna Ganduje ya jinjina ma shugaba Muhammadu Buhari

Zainab Aliyu
Source: Twitter

Zainab Aliyu ta tsallake rijiya da baya ne bayan mahaifinta ya dage kai da fata cewa bata da hannu a laifin da ake tuhumarta a kasar Saudiyya na safarar kwayar Tramol, inda daga bisani aka gano wasu baragurbin ma’aikatan filin sauka da tashin jirgin sama na jahar Kano ne suka sanya mata kwayar a cikin kayanta.

Ganduje yace binciken da NDLEA ta gudanar daya wanke Zainab daga wannan zargi ya tabbatar akwai miyagun ma’aikata a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano dake harkar safarar kwayoyi.

Haka zalika gwamnan ya bayyana farin cikinsa game da labarin daya samu na cewa akwai wani mutum guda dan Najeriya wanda shima aka sanya ma kwayoyi a cikin kayansa, kuma a yanzu za’a sakoshi daga gidan yarin Saudiyya a ranar Laraba.

Bugu da kari gwamnan ya jinjina ma ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami, ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ministan sufurin jirgin sama, Hadi Sirika, hadimar shugaban kasa akan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri da kuma ofishin jakadancin Najeriya a kasar Saudiyya saboda rawar da suka taka wajen sako mutanen biyu.

Daga karshe Gwamna Ganduje ya yi kira ga jama’a dasu kasance masu lura da kayansu a duk lokacin da suka shiga filayen sauka da tashin jiragen Najeriya don kare kansu daga sharrin miyagu da gurbatattun ma’aikata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel