Gwamnatin tarayya na kashe N17bn duk shekara wajen ciyar da Fursunoni

Gwamnatin tarayya na kashe N17bn duk shekara wajen ciyar da Fursunoni

Wani rahoto daga jaridar Leadership ya nuna cewa gwamnatin tarayya na kashe naira biliyan 17 duk shekara wajen ciyar da masu laifi da fursunoni da ke fuskantar shari’a a fadin gidajen kurkuku 244 da ke kasar.

Kwanturola Janar, na hukumar fursunan Najeriya, Ahmed Ja’afaru yayinda yake jawabi kan kasafin kudin 2018, a gaban mambobin majalisar dattawa kan harkokin cikin gida, ya bayyana cewa an tura naira biliyan 17 don ciyar da fursunoni.

Haka zalika, kakakin rundunar fursunan na jihar Abia, Ikpe Linus, ya gabatar da cewa yawan fursunonin da ke kasar ya tasar ma 72,000, don haka gwamnatin tarayya na kashe akalla N33,878,700 a kullun domin ciyar da fursunoni sau uku a rana akan N450.

Gwamnatin tarayya na kashe N17bn duk shekara wajen ciyar da Fursunoni

Gwamnatin tarayya na kashe N17bn duk shekara wajen ciyar da Fursunoni
Source: Depositphotos

Koda dai Linus ya sanya adadin fursunoni a fadin kasr a matsayin 73,786, wanda suka hada da maza 72,286 da kuma mata 1,500, rahoto ya nuna cewaa kimanin kaso 61 na jiran shari’a ne.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudi: Yan majalisu sun sanar da ranar mayar ma Buhari kundin kasafin kudin 2019

Da N450 da ake ciyar dasu a kullun, naira biliyan 17 ya kama kudin ciyar da fursunoni 73,786 duk shekara, mafi akasarin fursunonin a jiran shari’a ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel