Matasan Kogi sun tara N2m domin tazarcen Bello

Matasan Kogi sun tara N2m domin tazarcen Bello

Matasa daga fadin kananan hukumomi 21 na jihar Kogi karkashin inuwar kungiyar National Youth Council of Nigeria (NYCN) sun tara naira miliyan biyu ga Gwamna Yahaya Bello dmin ya samu damar siyan fam din takarar zaben gwamna wanda za a yi a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Shugaban kungiyar, Kwamrad Abdullahi Adamu, wanda ya bayar da tallafin kudin a gidan gwamnati a Lokoja a jiya Talata, 30 ga watan Afrilu, yace yunkurin na daga cikin burin matasa na ganin jihar Koi ta ci gaba da amfanuwa daga kyawawan shiri na gwamnati mai ci domin ci gaban jihar baki daya.

Adamu ya nusar da cewa jajircewar gwamnati mai mulki domin tabbatar da makoma mai kyau ga matasa a jihar abune mai matukar muhimmanci.

Matasan Kogi sun tara N2m domin tazarcen Bello

Matasan Kogi sun tara N2m domin tazarcen Bello
Source: Facebook

Ya yaba ma gwamnatin Gwamna Bello kan tarin ci gaban da ta kawo a jihar waanda acewarsa shineyasa mutanen jihar ke fatan ya sake takara, cewa yana da matukar muhimmanci kare martabar Kogi a karkashin gwamnatin APC.

Ya kuma bukaci gwamnan da ya mayar da hankali wajen inganta jihar ba tare da la’akari da sukar magauta ba, inda ua bashi tabbaci tara masa matasa a dukkanin yankunan jihar domin su zabe sa a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: Wani babban banki zai maidawa Gwamnatin Buhari Miliyan 40

Da yake martani, gwamnan ya yi godiya ga matasa akan jajircewarsu wajen ba gwamnatinsa goyon baya, cewa hakan ya nuna ainahin abunda matasa ke muradi a jihar Kogi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel