Wani babban banki zai maidawa Gwamnatin Buhari Miliyan 40

Wani babban banki zai maidawa Gwamnatin Buhari Miliyan 40

Wani kwamiti na musamman da ke kokarin zakulo kadarori da duk wani dukiyar gwamnati da ke hannun jama’a, SPIP, ya bayyana cewa ya samu sama da Naira miliyan 40 a wani banki da ke kasar.

Kwamitin na SPIP yayi wannan jawabi ne a Ranar Talata 30 ga Watan Afrilun nan. Shugaban harkokin sadarwa na wannan kwamiti, Lucie-Ann Laha, ita ce ta bayyanawa menama labarai wannan a wani jawabi da ta fitar jiya.

Lucie-Ann Laha take cewa binciken da su kayi ya sa sun gano kudi har Naira miliyan 40 ne a cikin wani babban banki, amma kuma kwamitin ya ki bayyana sunan wannan banki da aka samu da kudin gwamnatin tarayya a ciki.

Wannan kwamiti yayi bincike ne na musamman a game da yadda hukumomin gwamnatin kasar su rika gudanar da ayyukansu tsakanin shekarar 2019 zuwa 2015. Kwamitin yayi aiki ne da kwararru domin bankado irin wannan asiri

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta bada dama a kara bude wasu Bankuna

Wani babban banki zai maidawa Gwamnatin Buhari Miliyan 40
Shugaban Kwamitin SPIP da Gwamnatin Buhari ta kafa
Asali: Facebook

Binciken SPIS ya ta’allaka ne wajen bin kadin ajiyar kudin gwamnati da aka bada a cikin bankunan kasuwa domin gano ko ana zaftare kudin ko kuma ana tara riba. Tun a farkon shekarar nan ne kwamitin ya fara binciken.

Kwamitin ya gano cewa an sa wasu kudi da su ka hada da; N230,1444,784,34, da N180,932,793.39K da kuma wasu $161,350,79 a cikin wani asusun wannan banki, wanda a karshe kuma ba a maidawa gwamnati duka kudin na ta ba.

Wannan ya sa wannan kwamiti yayi maza ya bada umarni ga bankin ya dauki kudi N40,336.186.25k da kuma wasu Dala 56,919.10 ya maida cikin asusun bai-daya na gwamnatin Najeriya na TSA.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel