Ba za muyi murnar sakin Zainab ba har sai Buhari ya kubutar da Leah – kungiyar CAN

Ba za muyi murnar sakin Zainab ba har sai Buhari ya kubutar da Leah – kungiyar CAN

Kungiyar kiristocin Najeriya reshen Arewa ta bayyana rashin jin dadinta da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi gaggawar kokarin ceto Zainab, amma yayi biris tare da nuna halin ko in kula da Leah Sharibu.

Kaakakin kungiyar, kuma shugaban kungiyar kiristocin Najeriya reshen jahar Kaduna, Joseph Hayab ne ya bayyana haka a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu, inda yace abin takaic ne yadda yan Najeriya da basu ji ba, basu gani ba, ke shan wahala a kasashen waje.

KU KARANTA: Goje ya dau alwashin kin janyewa daga neman shugabancin majalisa har sai Buhari ya lallashe shi

Ba za muyi murnar sakin Zainab ba har sai Buhari ya kubutar da Leah – kungiyar CAN

Ba za muyi murnar sakin Zainab ba har sai Buhari ya kubutar da Leah – kungiyar CAN
Source: UGC

Ita dai Zainab Aliyu ta tsallake rijiya da baya ne bayan mahaifinta ya dage kai da fata cewa bata da hannu a laifin da ake tuhumarta a kasar Saudiyya na safarar kwayar Tramol zuwa kasar, inda daga bisani aka gano wasu baragurbin ma’aikatan filin sauka da tashin jirgin sama na jahar Kano ne suka sanya mata kwayar a cikin kayanta.

Yayin da Leah Sharibu dalibar makarantar yan mata dake garin Dapchi na jahar Yobe take hannun kungiyar Boko Haram fiye da shekara daya, bayan sun bukaci ta Musulunta amma ta ki.

Da wannan ne CAN take yaba ma gwamnatin tarayya game da hanzarin da tayi wajen ceto Zainab Aliyu, don haka ta nemi gwamnatin Buhari ta sanya irin wannan hanzari da muhimmanci wajen ceto Leah Sharibu daga hannun Boko Haram.

“Amma duk da wannan nasara da gwamnati ta samu, muna da tambaya, anya kuwa duk yan Najeriya daya muke a idon gwamnantin nan kuwa ko kuwa wasu sun fi wasu ne? banga dalilin murnar sako Zainab ba, amma mu yi biris da Leah wanda take hannun Boko Haram ba tare da aikata laifin komai ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel