Kasafin kudi: Yan majalisu sun sanar da ranar mayar ma Buhari kundin kasafin kudin 2019

Kasafin kudi: Yan majalisu sun sanar da ranar mayar ma Buhari kundin kasafin kudin 2019

Majalisar dokokin Najeriya ta sanar da ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu a matsayin ranar da zata mayar ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da kwaskwararren daftarin kasafin kudin shekarar 2019 bayan ta kammala aikin tantanceshi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai, Mustapha Dawaki ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata 30 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: An bayyana miliyoyin nairorin da iyalan shugaban UBEC suka biya kafin ya fito daga hannun masu garkuwa

Kasafin kudi: Yan majalisu sun sanar da ranar mayar ma Buhari kundin kasafin kudin 2019

Buhari
Source: UGC

Shi dai kasafin kudi ministoci da shuwagabannin hukumomin gwamnati ke shiryashi, daga nan sai bangaren zartarwa ta mika daftarin kasafin kudin zuwa ga majalisar dokoki, wanda zasu tantance ingancin alkalumman kudade da kuma na ayyukan da za’ayi dasu dake cikin kasafin, idan sun gama sais u mayar ma shugaban kasa ko gwamna ya rattafa hannu idan ya gamsu dashi kafin a fara aiwatarwa.

Dawaki ya danganta tsaikon da aka samu wajen daukn tsawon lokaci kafin su kammala aikin tantance kasafin kudin ga rashin grufanar wasu ministoci da shuwagabannin hukumomin gwamnati gaban majalisar don kare kasafin kudinsu a lokacin daya kamata.

“Kamar yadda kuka sani a yau muka kammala aikin kasafin kudi na 2019 daya kai naira tiriliyan 8.916, kuma zamu mikashi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis don ya rattafa hannu akai.

“A ranar 18 ga watan Disambar 2018 ne shugaba Buhari ya mika ma majalisa wannan kasafin kudi na naira Tiriliyan 8.86, kuma ya nemi mu hanzarta kammala aikin tabbatar da kasafin kudin zuwa karshe watan Maris, amma hakan bai yiwu ba saboda wasu ministoci da shuwagabannin hukumomin gwamnati sun ki amincewa su bayyana gabanmu don kare kasafinsu” Inji shi.

Daga karshe yace karin naira biliyan goma da majalisar tayi ma kasafin kudin Buhari sun yi ne domin samar da isassun kudade don yaki da ayyukan miyagun yan bindiga a jahar Zamfara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel