Gwamnatin tarayya ta kashe N3.5trn wurin ayyukan gine-ginen raya kasa a shekara 3, inji Osinbajo

Gwamnatin tarayya ta kashe N3.5trn wurin ayyukan gine-ginen raya kasa a shekara 3, inji Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo yace Najeriya na samu cigaba a bangaren masu zuwa saka hannun jari

- An samu karin kashi 37 cikin dari na bunkasar harkokin kasuwancin a Najeriya, kamar yadda mataimakin shugaban kasa ya bayyana

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya shaidawa manema labarai ranar Litinin a Abuja cewa gwamnatin tarayya ta kashe naira triliyan 3.5 daga kasafin kudi kan ayyuka gina kasa a shekara uku.

Mataimakin shugaban kasar yace masu hannun jari na kara matsowa kusa da harkokin Najeriya saboda wannan gwamnati ta basu damar yin hakan wanda ya sa hanyoyin kasuwanci ya karu da kashi 37 cikin dari daga shekarar 2017 zuwa 2018.

Gwamnatin tarayya ta kashe N3.5trn wurin ayyukan gine-ginen raya kasa a shekara 3, inji Osinbajo

Gwamnatin tarayya ta kashe N3.5trn wurin ayyukan gine-ginen raya kasa a shekara 3, inji Osinbajo
Source: Facebook

KU KARANTA:‘Yan bingida sunyi awon gaba da mataimakin rajistaran jami’ar jihar Taraba

Da yake magana wajen taron cigaban tattalin arziki na farko tsakanin kasashen Najeriya da Ingila wanda ya gudana a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja, Osinbajo yace tabbas akwai gagarumar cigaba fanni yin kasuwanci musamman ta bangaren masu saka hannun jari.

Wannan taro akan cigaban tattalin arziki dai an sanya mashi hannu ne a watan Ogustan shekarar 2018 wanda shugaba Buhari da Theresa May suka yi a birnin Landan domin karfafa tattalin arziki da kuma cigaban Najeriya da Ingila.

A cewar Osinbajo, “ Mun samu karin masu shigowa kasarmu domin zuba hannun jari da kimanin $90.9bn a shekarar 2018 wanda ya karu da kashi 37 cikin dari akan $66.4bn wanda muke dashi a shekarar 2017.” inji mataimakin shugaban kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel