Babu kanshin gaskiya a zargin yunkurin sauya kayan zabe – Inji INEC

Babu kanshin gaskiya a zargin yunkurin sauya kayan zabe – Inji INEC

Hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya, INEC ta karyata zargin ta da ake yi na cewa tana kokarin yin rufa-rufa na murdewa jam’iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari zaben da ya gabata.

Kamar yadda mu ka samu labari, hukumar ta INEC ta maidawa PDP martani ne ta bakin babban Sakataren ta na yada labarai, Rotimi Oyekanmi. Oyekanmi ne ya fitar da jawabi mai tsauri a matsayin raddi ga jam’iyyar PDP.

Rotimi Oyekanmi ya bayyana cewa babu abin da zai sa hukumar INEC ta biyewa jam’iyyar PDP a game da zargin murde zaben 2019 ganin cewa batun na kotu.Sai dai duk da haka INEC tace zargin da PDP ta ke jefawa sharri ne.

KU KARANTA: 2023: Ana zargin Tinubu da shirin tsige Shugaba Buhari daga mulki

Babu kanshin gaskiya a zargin yunkurin sauya kayan zabe – Inji INEC

Hukumar INEC ta musanya cewa an murdewa Atiku zabe
Source: UGC

Oyekanmi yana maida martani a game da maganar cewa INEC na kokarin sauya na’urorin da aka yi amfani da su wajen tattara sakamakon kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa na bana, inda yace wannan zargi sam bai da tushe.

INEC ta ke cewa bai kamata jam’iyyar ta rika jefa irin wannan zargi na karya ba don haka ta nemi jam’iyyar adawar da ta maida karfin ta wajen kare zargin da ta maka a gaban kotun sauraron karar zabe a madadin wannan surutu da ta ke yi.

Hukumar ta tsaya a kan bakar ta na cewa ba za ta rika maidawa jam’iyyar hamayyar martani kan abin da ta fada ba domin za su hadu a kotu domin gane mai gaskiya. PDP dai tana zargin INEC da taimakawa APC wajen murde zaben bana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel