Takardan shedan cin zabe: Okorocha ya ziyarci kotu a Abuja

Takardan shedan cin zabe: Okorocha ya ziyarci kotu a Abuja

Gwamna Rochas Okorocha na Jihar Imo ya ziyarci babban kotun tarayya da ke baban birnin tarayya Abuja saboda jinkirin da aka samu na sauya alkalin da zai saurari karar da ya shigar na rashin bashi takardan shedan cin zabe da INEC ta ki yi.

Okorocha ya isa kotun misalin karfe 4:20 na yammacin Talata tare da wasu hadimansa inda ya shiga ofishin mataimakin rajistara na kotun inda suka gana da misalin sa'a guda.

Okorocha wanda shine dan takarar sanatan jam'iyyar APC a zaben yankin Imo ta Yamma ya shigar da hukumar zabe INEC kara inda ya ke bukatar kotu ta tilastawa INEC mika masa takardan shedan cin zabe saboda baturen zabe ya sanar da cewa shine ya yi nasara.

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Takardan shedan cin zabe: Okorocha ya ziyarci kotu a Abuja

Takardan shedan cin zabe: Okorocha ya ziyarci kotu a Abuja
Source: Getty Images

Gwamnan ya kuma yi kara a kan Babban Alkalin Kotun, Mai shari'a Abdu Kafarati saboda canja alkalin da ke sauraron karar daga hannun Mai Shari'a Taiwo Taiwo zuwa wurin Mai shari'a Okon Abang.

Dan takarar jam'iyyar PDP, Jones Onyeriri da na jam'iyyar APGA, Osita Izunaso sun shigar da kara inda suke neman Mai shari'a Taiwa ya janye hannunsa daga shari'ar inda a cewar lauyan jam'iyyar APGA, Orji Nwafor Orizu "Mai shari'an yana goyon bayan wanda ya shigar da karar wato (Okorocha)."

Kafin dakatar da karar, 'yan takarar jam'iyyu guda hudu da suka hada da Nwachukwu Goodluck Clement na KOWA Party; Uche Onyeoma Ibe na Labour Party; Precious Nwadike na United Progressive Party (UPP) da Izunaso na APGA duk sun ce ba su amince kotun ta saurari karar ba.

Jam'iyyun sun zargi Okorocha da tilastawa baturen zabe sanar da cewa shine ya lashe zaben kuma suka kara da cewa kotun sauraron karrarakin zabe ce kawai za ta iya warware matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel