An kone wani mutum da aka kama yana yunkurin sace wani yaro a Bayelsa

An kone wani mutum da aka kama yana yunkurin sace wani yaro a Bayelsa

Wasu maza uku masu matsaikacin shekaru sun gamu da ajalinsu a ranar Talata bisa ikirarin da akayi na cewa sun sace wani yaro a garin Edepie da ke Yenagoa a jihar Bayelsa.

Lamarin ya afku ne a makarantar kudi da yaron ya ke karatu inda suka sace shi amma dubun su ta cika yayin da suka isa mahadar zuwa makarantar kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito.

A yayin da daya daga cikinsu ya gamu da ajalinsa sakamakon dukkan da mafusatan matasa su kayi masa, saura biyun sun tsira da kyar bayan 'yan sanda sun zo sun cece su.

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

An kone wani mutum da aka kama yana yunkurin sace wani yaro a Bayelsa

An kone wani mutum da aka kama yana yunkurin sace wani yaro a Bayelsa
Source: Twitter

Daya daga cikinsu ya amsa laifinsa inda ya ce wani dan siyasa ne ya basu kwangilar sato yaro wadda hakan ya kara harzuka mafusatan matasan.

Dukkan yunkurin da akayi na ji ta bakin rundunar 'yan sandan jihar bisa yadda matasa ke daukan doka a hannunsu bai yiwa ba saboda kakakin rundunar bai amsa wayarsa ba.

Wannan dai ba shine karo na farko da matasa da daukan doka a hannunsu ba idan an samu mai laifi a maimakon mika sa ga hukuma sai kawai ayi da dukkansa har wasu lokutan da kai ga rasa rayyuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel