Majalisar Dattawa za ta gudanar da bincike game da nadin sabon shugaban NYSC

Majalisar Dattawa za ta gudanar da bincike game da nadin sabon shugaban NYSC

Majalisar Dattawa ta umurci kwamitin ta na Wasanni da cigaban matasa ya gudanar da bincike dangane da nadin sabon shugban Hukumar Kula da Matasa masu yiwa kasa hidima, NYSC da Shugaban Hafsin Sojoji, Tukur Buratai ya yi.

A cikin 'yan kwanankin nan ne Buratai ya nadi Sani Ibrahim a matsayin shugaban NYSC domin maye gurbin Sule Kazaure.

An bukaci kwamitin da aka bawa alhakin gudanar da binciken ya gabatar da sakamakon bincikensa a ranar Laraba ta mako mai zuwa.

Majalisar Dattawa tayi korafi kan nadin sabon shugaban NYSC

Majalisar Dattawa tayi korafi kan nadin sabon shugaban NYSC
Source: UGC

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

An bukaci kwamitin ta bincika ta gani ko an saba doka wurin nadin sabon shugaban na NYSC.

An bayar da umurnin gudanar da binciken ne sakamakon korafi da Sanata Dino Melaye ya yi a kan batun.

Sanatan ya yi ikirarin cewa nadin da akayi ya sabawa dokar da ta kafa hukumar.

Ya ce, "Sashi 5 na dokar NYSC ya ce shugaban kasa ne ke da hurumin nadin shugaban hukumar da ake yiwa lakabi da Direkta-Janar.

"Abin mamaki kuma sai gashi shugaban hafsin sojoji ya tsige Direkta-Janar mai ci ya kuma nada wani sabo.

"Doka bata bawa kowa ikon nada shugaban NYSC ba illa shugaban kasa. Shugabanin kasa ne suka nada tsohon Direkta-Janar da wadanda suka shugabancin hukumar a bayansa.

"Idan muka bari haka ya cigaba da faruwa, shugaban FRSC ne zai nada shugaban majalisar dattawa kuma ya canja shi idan akwai bukatar hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel