Ruftawar gini ta raunata Mutane 8 a garin Ibadan

Ruftawar gini ta raunata Mutane 8 a garin Ibadan

Mun samu rahoton cewa, wani gini mai hawa biyu da ba a kammala ginin sa ba ya rufta a ranar Talata cikin birnin Ibadan na jihar Oyo inda ya murkushe Mutane takwas da suka samu munanan raunuka daban-daban.

Katafaren ginin da ke unguwar Jericho daura da babbar hanyar Eleyele a birnin Ibadan ya zube da misalin karfe 4.30 na Yammacin Talata kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ruftawar gini ta raunata Mutane 8 a garin Ibadan

Ruftawar gini ta raunata Mutane 8 a garin Ibadan
Source: UGC

Yayin ganawar sa da manema labarai, daya daga cikin maginan, Mista Kazeem Adebayo, ya ce zagwanyar kankare na wani bangaren ginin ce ta haddasa ruftawar sa baki daya ba tare da an farga ba.

Makamancin wannan hatsari ya auku a yankin Sogoye na birnin Ibadan inda wani gini mai hawa uku ya rufta a ranar 15 ga watan Maris. Kazalika a shekarar 2012 da ta gabata mutane shida sun jikkata yayin da wani gine ya rufta a karamar hukumar Oluyole ta jihar Oyo.

KARANTA KUMA: El Zakzaky da Matar sa na bukatar a duba lafiyar su cikin gaggawa a kasar waje - Likitoci

Cikin wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, aukuwar wasu munanan hadurra biyu ta salwantar da rayukan mutane 12 a a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel