Rundunar 'yan sanda tayi karin bayani a kan sakin shugaban hukumar UBEC, Dakta Mahmood

Rundunar 'yan sanda tayi karin bayani a kan sakin shugaban hukumar UBEC, Dakta Mahmood

A ranar Talata ne rahotanni suka bayyana cewar masu garkuwa da mutane sun sako shugaban hukumar ilimin bai daya ta kasa (UBEC), Dakta Mohammed Mahmood, wanda aka sace tare da diyar sa, Yesmin, a hanyar su ta zuwa Abuja.

Wata majiya ta bayyana cewar sai da iyalin Dakta Mahmood suka bayar da miliyan N13 a matsayin kudin fansa kafin a sake shi tare da diyar sa.

A nata bangaren, rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewar masu garkuwa da mutanen sun saki Dakta Mahmood tare da diyar sa, Yesmin, a yau.

Rundunar 'yan sandan ta kara da cewa ta kama wani mutum guda dake da alaka da sace Dakta Mahood tare da samun nasarar kwace wata bindiga kirar AK47. Kazalika, ta ce tana gudanar da bincike a kan lamarin.

Rundunar 'yan sanda tayi karin bayani a kan sakin shugaban hukumar UBEC, Dakta Mahmood
Shugaban hukumar UBEC, Dakta Mahmood, tare da diyar sa, Yesmin
Source: Twitter

Dakta Mahmood, na daga cikin dumbin mutane da 'yan bindig suka sace a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da rana.

Wata majiya dake da kusanci da Datka Mahmood ta shaida wa majiyar mu cewar an sace shi ne tare da diyar sa a hanyar su ta zuwa Abuja.

DUBA WANNAN: Dogara ya bukaci a kama shugaban hukumar RMAFC

Rahotannin sun bayyana cewar masu garkuwa da mutanen sun harbe direbansa, wanda nan take ya mutu.

Wani shaidar gani da ido, Mohammed Dambatta, wanda ya sha da kyar, ya shaida wa majiyar mu cewar masu garkuwa da mutanen sun sace mutane da dama a daidai Kurmin Kare a karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel