Hadurra biyu sun salwantar da rayuka 12 a jihar Adamawa

Hadurra biyu sun salwantar da rayuka 12 a jihar Adamawa

Aukuwar wasu munanan hadurra biyu a kan babbar hanyar Ngurore zuwa Mayo-Belwa, ta katse hanzarin Mutane 13 yayin da Mutane 21 suka jikkata a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Majiyar rahoton kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito ta bayyana cewa, hatsarin farko ya auku ne a daren ranar Litinin din da ta gabata inda rayukan Mutane shida suka salwanta yayin da mutane uku suka samu munanan raunuka.

Hadurra sun salwantar da rayuka 12 a jihar Adamawa

Hadurra sun salwantar da rayuka 12 a jihar Adamawa
Source: Depositphotos

Jami'in hulda da al'umma na karamar hukumar Mayo-Belwa, Kabiru Kelly, ya ce aukuwar hatsarin ta hadar da wata motar haya kirar Sharon yayin da direban ta ya yi yunkurin kaucewa wani rami inda nan da nan mai aukuwar ta auku.

An killace gawar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a asibitin birnin Yola yayin da ake ci gaba da jinyar wadanda suka jikkata a babban asibitin garin Mayo-Belwa.

KARANTA KUMA: El Zakzaky da Matar sa na bukatar a duba lafiyar su cikin gaggawa a kasar waje - Likitoci

Kabiru ya bayyana cewa hatsari na biyu ya auku yayin da wasu motoci biyu kirar Hummer da kuma Toyota starlet suka gwabzawa junan su inda nan take fasijojin daya daga cikin motocin biyu da suka hadar da Miji da Mata da kuma 'ya'yan su hudu suka ce ga garin ku nan.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hatsarin ya auku a yayin da matafiyan ke kan hanyar su ta zuwa jihar Zamfara daga birnin Jalingo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel